ƘAULANIN SAUYIN KUƊI: Kabiru Yusuf Anka

0
112

 

 

Shahararren marubuci Kabiru Yasuf Anka ya yi tambaya ga Gwamnatin Buhari game da canjin kudi. Marubucin ya wallafa  tambayoyin ne a shafin sa na Facebook Inda ya ke cewa..

Gwamnatin Buhari ta sanya wasu sharuɗa na sauya kuɗi, ciki har da lokacin daina karɓar tsofaffin kuɗaɗen.

Kuma tunin lokacin bayyanar sabbin kuɗaɗen da aka yi suka yi, aka fara sako su.

Amma wani abin mamaki, gwamnati tana biyan albashi da tsoffin kuɗaɗe, kuma suna zuwa ƙal-ƙal da su.

(1) Anya an shiryawa wannan sauyin kuɗin kuwa?

(2) Anya ba wasu za a cutar ba kuwa?

Tabbas akwai wata a ƙasa, fatanmu Allah ya sa kar talakawa su cutu a wannan harka, amin.

Leave a Reply