Ƙungiyar ƙallon ƙafa ta ƙara yin fintinkau bayan da ta lallasa ƙungiyar Wolves.

0
41

 

Daga Abu Usaimin

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta cigaba da ɗare teburin gasar firimiyar Ingila bayan da ta je har gida ta casa ƙungiyar Wolves da ci biyu da nema, a filin wasanta. A yanzu haka tazarar maki biyar ce a tsakaninta da mai bi mata wato Manchester city.

A cikin mintuna na 54 ƙungiyar ta jefa ƙwallonta na farko bisa gudunmawar ɗanwasanta mai suna Martin Odegard.

Duk da matsin labbar da suka fuskanta, hakan bai hana kocin Arsenal ɗin wato Arteta tare tawagar tasa yin nasara ba.

Nasarar da suka samu a daren ranar Asabar ita ce ta janyo kasantuwar ƙungiyar a mataki na ɗaya da maki 37 yayin da aka tafi hutun gasar cin kofin duniya ta ƙasa da ƙasa.

A ɗaya ɓangaren kuma, ƙungiyar Man city sun gaza ci gaba da matsin lambar da suke yi wa Arsenal bayan da suka sha kashi a hannun ƙungiyar Brentford. A yanzu haka suna mataki na biyu da maki 32.

Liverpool  sun cigaba da zama a mataki na 6 bayan ta lallasa Southampton da ci 3 da 1 a filinsu mai suna Anfield.

Tottenham kuwa ta tsallake rijiya da baya, bayan ta ƙarƙare wasa da 4 da 3 tsakaninta da ƙungiyar Leeds.

Ƙoƙarin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ya samu tasgaro bayan da ta sake yin rashin nasara a karo na uku kenan a kakar bana.

Leave a Reply