Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester ta cire hotunan ɗan wasa Cristiano Ronaldo daga filin wasan ta na Old Trafford

0
122

Daga Abu Usaimin

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta fara ɗaukar mataki a kan ɗan wasanta na gaba mai suna Cristiano Ronaldo, bayan ya yi wasu kalamai a hirar da yi da fitaccen ɗan jaridar nan wato Piers Morgan. A hirar tasa da ya yi, ya taɓo ɓangarori da dama, wamda kuma kalaman nasa kai-tsaye suka taɓa muhibba ta ƙungiyar.

A wannan Larabar ne aka hango wasu ma’aikata na kyakkyeta hoton ɗanwasan da yake jikin babban allon da ke cikin filin wasan nasu mai suna Old Trafford.

Ɗan wasan mai shekaru 37 ya tabbatar da Piers Morgan a tattaunawar tasu, tabbas zai bar ƙungiyar saboda rashin jindaɗin hana shi tafiya da suka a baya.

Ya ce iyalan Glazer (masu ƙungiyar) ba su damu da cigaban harkokin wasa, sannan sun zarge shi da rashin martaba mai horarwarsu wato Eric Ten hag. Sannan kuma babu sauyi tun bayan barinsa ƙungiya a shekarar 2008.

A bayanan ƙungiyar na ranar Litinin “Ƙungiyar Manchester ta ci karo da wani bidiyo da aka tattauna da ɗan wasa Cristiano Ronaldo. Za mu yi martani bayan mun samu cikakkun bayanai. Za mu mayar da hankalinmu kan ƙarashen wasanninmu na kakar bana, da kuma samar fahimtar juna da haɗin kan da muka faro tun daga fari, tsakanin ma’aikata, ‘yan wasa da ma magoya bayanmu.”

Yanzu haka dai ƙungiyar ta fara yunƙurin ɗaukar mataki a kan ɗan wasan nata, ɗan asalin ƙasar Portugal, bayan da aka hango ma’aitan ƙungiyar suna cire hoton tallansa da ya yi wa kamfanin Adidas. Hoton da yake manne a babban allon filin wasan ƙungiyar.

Leave a Reply