Ɗalibi ya kashe abokinsa ɗalibi a jihar Bauchi

0
87

An kama  Kamaluddeen Musa mai shekaru 22, ɗalibi a kwalejin ilimi ta Adamu Tafawa Balewa da ke karamar hukumar Kangere-Bauchi bisa laifin kashe abokinsa  shi ma  ne ɗalibin makarantar sabida saɓani.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan SP Ahmed Mohammed Wakil ya bayyana hakan ga manema labarai a Bauchi.

Ya ce, “A ranar 28 ga watan Nuwamba, 2022 da misalin karfe ɗaya na rana, bayanan da rundunar ta samu sun nuna cewa a ranar da misalin karfe 9:15 na safe, Kamaluddeen Musa ya daɓa wa abokinsa Usman Umar wuƙa, mai shekaru 25 , a cikinsa.

Wakil ya ce lokacin da ‘yan sandan suka isa wurin; sun ɗauki wanda aka daɓa wuƙan, zuwa Asibitin ƙwararru na Bauchi, inda likitoci suka tabbatar da cewa ya mutu, yayin da nan take aka kama wanda ake zargin.

Ya ce, “Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wadanda ake zargin da wanda aka kashen abokanai ne kuma ɗaliban makarantar sakandare ta Adamu Tafawa Balewa College of Education Kangere, Bauchi LGA, Jihar Bauchi.

“Kuma a ranar 28 ga Nuwamba, 2022 da misalin karfe 09:15, an samu ‘yar hatsaniya a tsakanin su, a lokacin da marigayin ya yi kukan cewa wanda ake zargin ya fita ba tare da sanar da marigayin ba, lamarin da ya haifar da fada wanda ya yi sanadin rauni a yatsar wanda ake zargin, ana cikin haka sai wanda ake zargin ya zaro wata karamar wuka daga aljihunsa ya daɓa wa marigayin, a cikinsa.

Leave a Reply