Ɗan wasan ƙwallon ƙafa Bello Ƙofar mata ya kwanta dama

0
153

Idris Malikawa, jami’in yaɗa labarai na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars da ta koma mataki na biyu, ya bayyana kaɗuwarsa bisa rasuwar tsohon ɗan wasan ƙungiyar, Bello Kofarmata.

A cewar Malikawa, dan wasan wanda ke cikin tawagar Flying Eagles a gasar cin kofin duniya ta matasa ‘yan ƙasa da shekaru 20 ta Canada 2007, ya rasu ne a daren ranar Talata yana da shekaru 34, bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya a mahaifarsa a unguwar Kofar mata a ƙwaryar birnin Kano.

Ƙofarmata

Jami’in yaɗa labarai na ƙungiyar ya ce ‘Sai Masu Gida’, kamar yadda ake kiran Pillars, za su ci gaba da tunawa da ɗan wasan Super Eagles da ya mutu. “Ba abu ne mai sauƙi rasa matashin ɗan wasa ba, musamman wanda ya ba da gudummawa mai yawa ga nasarar ƙungiyar Kano Pillars. “Na tuna sarai a 2008, Bello yana cikin tawagar da ta lashe kofin NPFL na farko a kulob ɗin, za mu yi kewarsa, zai kasance har abada a cikin wannan kulob ɗin, ya kuma kasance cikin nasarorin da kulob ɗin ya samu a nahiyar a lokacin da muka kai wasan kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin zakarun Turai ta CAF.

“Babu yadda za a yi a kwatanta yadda ake jin rashin irin wannan ɗan wasa kamarsa.” inji shi.Malikawa ya ƙara da cewa, ba wai kawai marigayin ya taka rawar gani a matakin kulob ba, ya kuma yi a matakin ƙasa inda ya buga wasan U-20 da U-23.

Ya kuma samu gayyatar zuwa tawagar Eagles, ” sam ba za a manta da dattakun saba, ya fito daga gidan ‘yan ƙwallon ƙafa kuma ya kasance mai tawali’u da sauƙin kai, shi ya sa kulob ɗin ya karrama shi, kuma muka je aka yi jana’izarsa da mu sannan muka yiwa ‘yan uwansa ta’aziyya” inji shi.

Ƙofarmata ya koma Pillars ne a shekara ta 2007 kuma ya taimakawa ƙungiyar ta lashe kofin Firimiyar Najeriya a 2007/08 da kwallaye 11. Shi ne kuma wanda ya fi zura kwallaye a gasar a wannan kakar, ya kuma taka leda a Heartland, Elkanemi Warriors da kuma taka leda a kasashen waje tare da IK Start na Norway, ya buga wa Super Eagles wasa ɗaya, wasan sada zumunci da suka doke kasar DR Congo da ci 5-2 a Abuja a watan Maris na 2010.

Leave a Reply