2023: INEC ta yi fatali da dukkan sunayen waɗanda su ka yi rajistar zaɓe sau biyu -Okoye

0
188

 

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ta bayyana cewa ta yi fatali da sunayen waɗanda su ka yi rajistar zaɓe sau biyu masu yawa.

A nan, hukumar na magana ne kan waɗanda su ka yi rajista daga 15 ga Janairu zuwa 31 ga Yuli, 2022.

Kakakin Yaɗa Labaran hukumar, Festus Okoye ne ya bayyana haka a ranar Litinin, cikin wata sanarwar da ya raba wa kafafen yaɗa labarai.

Ya ce an tsame sunayen ta hanyar amfani da na’urar tantance rajistar sunayen da aka shigar fiye da sau ɗaya (ABIS).

Ya ce akwai ƙa’idojin da INEC ta shimfiɗa, waɗanda idan wanda ya yi rajista bai cika su daidai ba, to za a cire sunansa ne kawai.

Okoye ya ce an kammala aikin tsame sunayen, kuma nan ba da daɗewa ba za a bayyana waɗanda su ka yi rajista daidai, yayin da za a haɗa sunayen na su da sunayen waɗanda aka yi wa rajista a baya.

Daga nan ya ce za a fara rabon Katin Shaidar Rajista (PVC) a ƙarshen Oktoba da kuma farkon Nuwamba.

Idan za a iya tunawa, INEC ta ce waɗanda su ka yi rajista tsakanin Yuni 2021 zuwa Janairu 2022, su 2,523,458 ne, amma da ka tankaɗe waɗanda waɗanda ba su yi rajista daidai ba, an tsame sunaye 1,126,359.

A farkon Disamba ne dai INEC ta ce ta fara tsame sunayen waɗanda su ka yi rajista sau biyu ko fiye da haka.

A cikin labarin, an ruwaito Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana fara aikin tsame sunayen waɗanda su ka yi rajistar mallakar katin zaɓe sau biyu ko fiye da haka.

Shugaban INEC Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke jawabi a wurin taron masu ruwa da tsaki, kan bitar fayyace ƙa’idojin zaɓe a sansanin masu gudun hijira.

An shirya taron ne ranar Talata a Abuja, inda Yakubu ya ce sake nazarin tsare-tsaren ya zama wajibi, domin rabon da a sake bibiyar sa tun na ƙarshe da aka yi a 2018, kafin zaɓen 2019.

Ya ce ana nan ana ci gaba da tsame sunayen da aka yi rajista sau biyu ko fiye da haka ana zubarwa, domin a tabbatar da cikakkun adadin yawan waɗanda za su mallaki katin rajistar zaɓe guda ɗaya tilo, kamar yadda doka ta tanadar.

Ya ce sai an kammala tsame sunayen masu rajistar fiye da sau ɗaya sannan za a bayyana ranar da za a liƙa sunayen masu rajista, kowa ya gani a faɗin ƙasar nan.

“A tsarin ganin an gudanar da zaɓuka cikin sansanin ‘yan gudun hijira, mu na so mu tabbatar cewa wannan tsari kamar yadda doka ta tanadar, ba a bar kowa a baya ba.

“Za mu tabbatar kamar yadda dokar zaɓe ta shimfiɗa cewa an gudanar da zaɓe a sansanin masu gudun hijira, kuma naƙasassu sun samu damar yin zaɓe da kuma waɗanda wani Ibtila’i na barin gidajen su ya shafe su, kamar ambaliya.”

Yakubu ya ce aƙalla akwai mutane miliyan uku a sansanonin gudun hijira daban-daban a ƙasar nan.

Ya ce taron sake nazarin su ya zama wajibi a yanzu, saboda masu gudun hijira ɗin sun ƙaru, sakamakon wasu dalilai, kamar ambaliya.

Ya ce a yanzu kuma za a bayar da himma wajen ganin an wayar da kan mazauna sansanonin gudun hijira dangane da muhimmancin zaɓe da kuma ƙa’idojin da doka ta shimfiɗa wajen gudanar da zaɓe a cikin masu gudun hijira.

Shugaban INEC ya musanta zargin da Gamayyar Ƙungiyoyin Kare Haƙƙin Jama’a (CSO) su ka yi wa INEC cewa ta karya dokar Sashe na 19(1) na Dokar Zaɓe, sashen da ya fayyace yadda INEC za ta liƙa sunayen waɗanda su ka yi rajista, domin kowa ya gani a ƙasar nan.

“Ba mu karya wata doka ba. Saboda har yanzu ana kan tantancewa da tsame sunayen waɗanda su ka yi rajista sau biyu ko fiye da biyu tukunna. Idan lokacin da za mu liƙa sunayen ya yi, za mu sanar kowa ya sani, kuma ya gani.” Inji Yakubu.

Ya ce za a liƙa sunayen a dukkan mazaɓu 8,809 da ake da su a ƙasar nan a dukkan ƙananan hukumomi 774 a Nijeriya, kamar yadda Sashe na 19(1) na Dokar Zaɓe ta 2022 ya tanadar.

Ya ce za a haɗa sunayen da aka yi rajista a baya-bayan nan tare da adadin miliyan 84 da ake da su a baya.

Leave a Reply