Labarai

Tinubu da Shatima sun ɗauki rantsuwar kama aiki

 

Zuwa yanzu, zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Nigeria a tutar jamiyyar APC Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa sun ɗauki rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban ƙasar Nigeria mai cikakken iko da mataimakinsa a wani ƙwarya-ƙwaryan taro da ake gudanarwa a filin taro na Eagle square dake Abuja.

Taron ya samu halartar shugabannin ƙasashen Afirka da dama, da wakilan shugabannin ƙasashen Amurka, Kanada da Faransa.

Tsohon shugaban ƙasar Nigeria Muhammadu Buhari ne yake jagorantar bikin miƙa mulkin ga Bola Ahmed Tinubu tare da mataimakimsa a halin yanzu.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button