Labarai

Rarara ya ce zai ɗauki nauyin biyan albashi ga ‘yan sandan da aka kora

“Na tuntuɓi mutane daban-daban domin su shiga maganar, tun kafin a kore su, amma duk da shiga tsakani da rokon da na yi wa 'yan sanda, amma rundunar ta dage kan korar su,” in ji Rarara

Shahararren  mawakin  siyasar nan,  Dauda  Kahutu  Rarara, ya yi alkawarin  cigaba da ɗaukar nauyin ƴan sandan nan guda uku da rundunar “yan sandan Nijeriya ta kora bisa laifin harbi da bindiga ba  bisa ka’ida ba  da  kuma rashin sanin  makamar aiki.

A wani faifen bidiyo da mawaƙin ya saki a yanar gizo, Jaridar FASIHIYA ta ruwaito mawaƙin yana cewa “yan sandan da ke tsaron lafiyar sa sun shiga cikin matsala bayan wani faifan bidiyo da ya nuna yadda suke harba bindiga a sama, a wani mataki na nuna karfin tuwo ga abokan hamayyar sa.

Rundunar ‘yan sanda dai ta ce bayan bincike, ta samu Insp. Dahiru Shuaibu, Sgt. Abdullahi Badamasi da Sgt. Isah Danladi da laifi kuma daga baya ta sallame su daga aiki.

Da ya ke magantuwa a kan korar da aka yi musu, mawakin ya sha alwashin ci gaba da sauke nauyin da ke kan su da suka hada da biyan su albashinsu na wata- wata.

Sai dai ya ce ya na roko ga rundunar da ta yi musu sassauci.

Masu tsaron Rarara da aka kore

 

“Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kori jami’an tsaro na. Bayan sun sanar da ni sai na tambaye su ko nawa ne albashin su a ’yan sandan Najeriya, sai suka gaya mi ni.

“Kuma na yi masu alkawari cewa, daga yanzu, zan ci gaba da biyan su albashin da rundunar ‘yan sanda ke biyan su.

“Sun ɗaukaka ƙara kan korar da aka yi musu, kuma idan sun yi nasara, za a iya mayar da su bakin aiki, idan kuma a ƙarshe hakan bai faru ba, zan ci gaba da biyan su albashi.

“Na tuntuɓi mutane daban-daban domin su shiga maganar, tun kafin a kore su, amma duk da shiga tsakani da rokon da na yi wa ‘yan sanda, amma rundunar ta dage kan korar su,” in ji Rarara.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button