A  ranar haihuwata mahaifiya ta ta fada min cewa bata samu doguwar nakuda ba

0
285

 

Mahaifiya ta tana  sanar da ni abubuwa da dama  game da haihuwa ta.

Ta ce bayan ta idar da sallar la’asar ba.jimawa nakuda ta taso mata.ranar Juma’a ta shekarar 1982, ta ce kin iso Duniya cikin kuka mai karfi wanda ya nuna kina cikin koshin lafiya,  kuma har ake zaton ko da namiji ne, bayan an tabbatar da cewa mace aka samu sai mahaifinki ya dauke ki ya yi min a’ddu’a da huduba.

Halima K Mashi Jaririya

Ya ce An samu Halimatu Sadiya insha Allah za ta zama abin alfahari.
Mahaifiya tace ta samu alkhairi sosai a lokacin haihuwata. Ta fada min cewa kin taso da farin jini har ina  boye ki saboda bakin mutane kasancewar ki fara tas ga gashin kai.
Ta ce kin kasan ce mai d’afa kiwa bakya yarda kowa ya dauke ki amma baki da rigima.

Halima K Mashi ‘Yar Shekara Takwas

Ina jin dadin labaran kuruciya ta da mahaifiya ta ke bani musamman na lokutan da bazan tuna ba, wato daga haihuwa ta zuwa yaye ni daga shan Mama.

Na taso cikin gata da kula da soyayyar mahaifa kasancewar lokacin da aka haifeni ana sa ran cewa an daina Haihuwa. Na samu tarbiyya ban fuskaci kowace irin damuwa  ta  bangaren karatuna ko bukatuna na yau da kullum da zan iya tunawa ba, duk da kasancewar mahaifana ba attajirai bane masu rufin asiri ne da wadatar zuci.

Na soma fuskantar kalubalen rayuwa ne a lokacin da na cika shekara goma sha hudu da wata takwas a watan September’ 14 na 1996 aji daya a karamar sakandire lokacin da aka daura min aure…….

Na dakata a nan watarana zan rubuta tarihin rayuwa ta.

A duk lokacin da rana irin wannan ta zagayo ta haihuwata na kan samu kaina cikin yanayi kala uku.

Farin ciki damuwa da kuma fargaba. Ina Farin cikin na kara shekara a saman shekaru na ina godiya ga Ubangijin da ya bani damar ganin lokacin.

Tare da Mahaifiyar ta

Ina fargabar kila ba zan kuma ganin wata shekarar ba. Sannan ina damuwa game da laifuka da na aikata a shekarar da ta gabatar ba.

Ina taya kaina murnar zagayowar ranar Haihuwata ina fata inyi kyakykyawan karshe. In rabu da Mahaifiyata lafiya kamar yadda na rabu da mahaifina.
Ina fatan in hadu da mahaliccina cikin salama a ranar aminci.

Leave a Reply