ABU MAFI GIRMA DA DARAJA GA MACEN DA TA ƊAUKI MAI AIKI TA MATA TARBIYYA: SADIYA YAKASAI

0
113
Safiya Garba Yakasai

Shaharariyar marubuciyar nan Hajiya Sadiya Garba Yakasai ta bayyana mana ra ‘ayin ta game da ɗaukar ‘yar aiki da kuma dalilai da suke sa a ɗauki ‘yar aiki.

In baku manta ba a kwanakin baya ansu inda wata ‘yar aiki ta zuba maganin ƙwari a cikin abincin iyayen gidan ta, sannan an kuma samu wata da ta bayyana yadda take shan jinin matar da take yi wa aiki da yaran ta. Bisa ga wannan dalilin filin mu na yara da mata ya ya ji ta bakin marubuciyar don jin dalilin da ke janyo hakan.

Ga yadda ta fara da bamu tarihin ta a taƙaice.

Sunana sadiya Garba Yakasai. Anhaife ni cikin unguwar Yakasai Kan tudu Masallacin jalli. Na fito daga cikin zuriar Ibrahim Dabo, nayi karatun firamare da sakandire, nayi Diploma a fannin Girke-Girke da interiors na gida a garin Lagos, da na samu wannan damar lokacin aiki ya Kai Mijina can sai na mai da hankali a nan,daga baya na fada harkokin Rubuce Rubuce har yanzu ina taɓawa. Wannan shine takaitaccen tarihina.

Mun tambaye ta ko waɗanne dalilai suke sa mata su ɗauki ‘yar aiki sai ta ce..

“To zamu iya cewa akwai dalilai da dama da suke sa mata ɗaukar mai taimako. Ba lallai son rai ne yasa ba, wasu akwai yanayin aiki ne, wasu kuma ra’ayin ne hakan, wasu kuma gaskiya lalaci ne ko kuma samun dama. Amma da yawa Jin daɗi ne da kuma samun damar hakan yasa suke ɗauka.Sai kuma akuma Wasu da matsala ta rashin lafiya ko jinya.

Mun tambaye ta ko gallazawa ce ta ke saka yara ‘yan aiki su cutar da iyayen gidan su kamar yadda ake samu sai ta faɗa mana nata ra’ayin kamar haka.

Yana danganta da yanayin ɗan Adam, akan samu wasu matan masu saurin fushi da fusata, nan da nan sai su yi wa ‘yar aiki zavin cin zarafi har da duka, akan wannan sai kaga ‘yar aiki tana neman yadda zata ɗauki fansa. Wasu kuma halittar su ce hakan wato gallazawar wala Allah kan masu aikin ko akasin haka, wasu kuma kawai tsabar mugunta ce ko rashin hakuri da ganin kaman siyan yaran suka yi, dan su yi musu bauta.

Sannan suma masu aikin fa suna bawa iyayen gijin nasu damar hakan, da yawa basa jin magana kuma suna zaƙewa gurin shigewa maigida. ga sata. Kuma ana samun wasu suna gallazawa yaran iyayen gidan su ta fannoni da dama, kamar duka ko hana abinci aka lokaci in iyayen su basa nan.

Aganina ƙwaryar sama ce take dukan ta ƙasa amma iyayen gidan sun fi cusgunawa mai aiki shiyasa in suka horu suke zame musu ƙadangare bakin tulu anawa ganin kenan.

To ka ɗakko wanda baka sani ba ka bautar dashi ba dare ba rana, ka sakar masa ragamar gidan ka komai sune hatta makwancin miji mai aiki tana da damar shiga dole raini da ƙyashi ko makamancin haka ya shiga, in kin kasance kina azabtar da mai aiki lallai wataran zata ɗauki
doka a hannun ta ta cutar da iyalanki a matsayin ramuwa.

Amma idan kin kyautata mata sha Allah zata ɗauke ki da mutunci wasu kuma a rashin sani suke ɗaukar ‘yar kungiyar asiri,ko maiyya ,ko muguwa ba tare da sani ba, kafin ka gano wani abu ta gama illata ki.

Da muka tambaye ta ko suna bincike kafin su ɗauki “yar aiki sai ta ce..

Gaskiya da yawa ba wani bincike, wanda hakan bai kamata ana ɗaukan ‘yar aiki kai tsaye ba, ba tare da sanin wani nata ba, yin hakan babban kuskure ne amma mutane ba sa damuwa da hakan. Mafi akasari wata ce can zata kawo maki yarinyar wadda ita ma baki san asali ta ba bare yarinyar.

Da muka tambaye ta shawarar da zata ba mata in za su ɗauki mai aiki sai ta ce.

.Ki bincika kisan iyayenta da kuma asalin ta.Sannan ki zamo mai kyautatawa mai aikin ki in har ta zama dole sai kin ɗauka ɗin .Sannan abu mafi girma da daraja ga macen da ta ɗau mai aiki to ta koya mata irin rayuwar da take yi a gidan ta ba tare da tsangwama ba ko kyara, ko kuma mugunta, duk yadda zata ga girman ta to tayi ta kyautata mata don ƙulla alaƙa mai kyau tsakanin su har yadda zata tafiyar mata da yara cikin tarbiyya da kulawa.

Duk irin wannan da sakacin matar gida muddin taga take taken mai aiki bana arziki bane ko tana son shisshige wa mai gida ko yawan hanttarar Yara,to ta tsawatar kuma ta ja mata kunnen Yadda zata tafiyar mata da yara, idan taki kawai ta sallame ta sai a zauna lafiya.
Duk da cewa taimakon juna ne gaskiya tsakanin mai aiki da wacce ake wa aiki kowanne yana buƙatar ɗan uwansa. Ita ‘yar aiki dole tayi biyayya ta girmama uwargijiyar ta zata bata abinci da suttura har makaranta suna saka su, duk wanda ya yi ma haka ina ga ya wuce komai.

Leave a Reply