Abubuwan Da Za Su Iya Faruwa Da Ke Idan Ki Ka Daina Jima’i

0
66

 

Wasu saboda sun rabu da mazan su ne. Wasu mazan ba sa tare dasu. Wasu matan kuma haka nan kawai mazan su ke daina saduwa da su ko kuma su da kan su su nuna ba su da sha’awar Jima’i da mazajen su. Ko ma dai menene dalilin da ke hana ki samun biyan buƙata irin ta jima’i, ki na da naƙasu saboda rashin yin sa a lafiyar ki.

Kowace mace da irin haƙurin ta na tsawon lokacin da za ta iya ɗauka ba tare da jima’i ba.
A wannan darasin mun binciko muku illar da rashin jima’i ya ke haifar wa lafiyar duk wata mace da ta saba da shi yanzu kuma ba ta samun yi.

Da zaran mace ta daina samun jima’i kamar yadda ya kamata za a same ta da yawan fushi, da kuma kasala. Haka nan kawai abu zai riƙa bata mata rai ba tare da wani dalilin ba. Sannan a ko da yaushe jikin ta babu ƙarfi.

Baya ga hakan, masanan sun tabbatar da cewa rashin samun yin jima’i ga mata ya kan sa su saurin mantuwa da kuma disashen ƙwaƙwalwa.
Tunani da hankalin macen da ta ke yin jima’i ya fi na wacce ba ta samu.

Kamar su ma maza, matan da ba sa samun gudanar da jima’i a kai a kai a yawancin lokuta su na cikin cuta. Ciwo mai sauƙi irin mura idan ya kamata macen da ba ta samun sabis sai ya jima bai warke ba. Amma macen da ta ke samu nan take ya ke ɓacewa.
Kamuwa da cutuka cikin sauƙi ya fi addabar macen da ba ta jima’i.

Farjin macen da ba ta samun jima’i zai tsuke, ƙofar gaban ta za ta dawo ƙarama, yadda duk lokacin da za a sadu da ita sai ta ji ciwo.

Haka nan macen da ba a yawan saduwa da ita ta na iya fuskantar bushewar farjin ta ko kuma zubar ruwa a gaban ta a wasu lokutan.
Macen da ba ta samun namiji a duk lokacin da za ta yi al’ada sai ta zo mata da zafi da kuma ciwo ba kamar macen da ta ke samu ba.

Idan mace ta ɗauki tsawon lokaci babu jima’i ta kan iya daina jin sha’awar jima’i a tare da ita. Za ta ji sha’awa ta ɗauke mata. Duk wannan illar rashin sabis ke kawo su.

‘Cardiovascular’ wata cuta ce, inji masana, da ke iya kama duk wata mace da ta jima ba ta hau netwok ba. Su ka ce shi yawan saduwa ga ɗiya mace ya kan taimaka mata wajen kuɓuta daga kamuwa da cutar zuciya.

Duk da waɗannan matsaloli ne da rashin samun jima’i kan iya haifarwa ga lafiyan mace. Akwai kuma wasu alfanun da mutum zai iya samu idan ya daina jima’i inji su masanan. Waɗanda nan gaba za mu kawo su idan Allah ya ba mu ikon.

Yanzu dai maza da mata kun ji illar da rashin jima’i ke iya jawo wa ɗan’adam ga lafiyar sa. Da fatan za a bi hanyoyi na halas wajen yin jima’in a kai a kai.

* Malam Tonga marubuci ne da ke Kaduna.
#TsangayarMalam

Leave a Reply