A kwai dalilan da ke sa matan aure bin maza: Sa’adatu Saminu kankiya

0
522
Marubuciya Sa'adatu Saminu kankiya

Jaridar Fasihiya ta tattauna da shaharariyar marubuciyar nan Sa”adatu Saminu Kankiya.

filin mu na Mata A yau mun tattauna da marubuciyar ne a kan matsalar nan da ta addabi mata, wato  yadda maza suke matsa wa mata, ba sa ɗauke kan su sai sun latsa su a duk inda suka gan su.

A hirar mun ji nata ra’ayin inda tace sune dalilan da suke sa hakan ke faruwa.

Amma da  farko mun fara da jin taƙaitaccen tarihin ta kamar haka..

Sunana Saminu kankiya,ni haifaffar jihar Katsina ce ina zaune a ƙaramar hukumar kankia, ina cikin shekara ta 45 yanzu. Marubuciya kuma uwa. Na shiga harkar rubutu a 2002,nayi rubutu da yawa da suka shafi zamantakewar aure da soyayya.Kuma ni ma’aikaciya ce.

Mun tambaye ta dalilan da suke sa maza da sunga mata kamar kura ta ga nama. Sai ta ce..

“Wannan hali da muka samu kanmu ciki,sai dai muce “innalillahi wa’inna ilaihi raji’un! saboda wannan matsalar ta zama ruwan dare, ba ga manya ba ga yara ba,ga malamai ba ga jahilan ba, da yawan maza sun ɗauki wannan halayya sun sanya a zukatan su, kuma basu damu da kusancin su da matan ba abin da ɗaure kai matuƙa. Muddin mace bata bi a sannu ta sa tsoron Allah a zuciyar ta ba,to tabbas zata iya faɗawa tarkon irin waɗannan mazan da suke farauta mata kullum rana.

Wani abin takaici shine, mafi yawan maza masu irin wannan halayyar da zaka je ka tattauna da matan su zaka samu basu damu da haƙƙin matan ba, basu iya biya masu buƙata, amma saboda taɓewa sun zo waje suna neman duk wata mace da suka ƙyalla ido akanta,komin lalacewar ta komi kamun kanta.

Wani abin tashin hankalin shine,suna nan sun sanya ido suga miji ya mutu ya bar mace da ‘ya’ya, kwana kaɗan za’a shigo mata da shigar tausayawa za’a taimake ta,wallahi da an samu marar wayau sai su maida ita kamar matar su, wannan yazo wancan ya tafi.

Wannan fitinar tayi yawa,yana da kyau Malamai su miƙe tsaye,wajen fadakarwa ga maza da mata don samun sauƙin wannan masifa.”

Mun tambaye ta dalilan da take ganin ne suka janyo hakan. Sai ta ce.

Akwai mata masu kwaɗai da son abin duniya, sun ɗora ma rayuwar su dole sai sunji daɗi don haka ba su damu ba duk hanyar da za su shiga don su samu abinda suke baƙata za su shiga, ɗan abinda suke samu shi yake rufe masu ido su shiga wannan harkar.

Akwai kuma waɗanda yanayin rayuwa ne ke sanya su shiga wannan halin, saboda muna cikin wani yanayi da taimako ya yi ƙaranci, za’abar mace da ‘ya’ya marayu amma kaf a cikin dangi sai a rasa wanda zai rinƙa taimaka masu, akwai matsalar abinci,kayan masaruf,i sutura, karatun yara da sauran hidimomin rayuwa na yau da kullum.
Duk an barsu a hannun mace, alhalin bata da sana’a ko aikin da zata yi waɗannan hidimomin,dole ta shiga waccan hanyar don ta samu yanda zatayi hidimomin rayuwarsu, wallahi wasu matan ma abokan mijin ko ‘yan uwan shi na jini ne ke fara zuwa su gurɓata masu rayuwa, sannan su taimake su.

A halin da ake ciki yanzu na tsadar rayuwa,sai mace mai ƙarfi sosai ce ke iya ɗaukar ɗawainiya ‘ya’yanta, wani ƙaramin jari baya iya riƙe mace, don haka zina ta yawaita a wajen zawarawa, saboda ita ce kaɗaice hanyar da mace zata bi a taimaka mata ta iya ɗaukar dawainiyar ‘ya’yanta.”

Mun tambaye ta game da matan aure da suke tsunduma kan su a cikin lamarin sai ta ce..

Matan aure kuma da ke bin maza waje,shima akwai dalilan da suka assasa

Sa’adatu Saminu kankiya

hakan ,akwai mata masu buri na ƙarya da dole sai munji daɗin da suke so, sun raina hidimar da mazansu suke yi masu, don haka sai su fita waje,ayi amfani dasu a basu kuɗi,su zo suyi waɗannan buƙatun.

A kwai kuma matan auren da mazan su ka banzatar da su basu tsare masu haƙƙinsu ,basu biya masu buƙatar su, kamar yanda nace, wasu na waje suke nema amma kuma basu iya biya ma na gida buƙatar su ba, ko lalura ta rashin lafiya,akwai kuma waɗanda shaiɗan ya rinjayi zukatan su mazan su suna tsaye akan su, amma kuma kullum idanuwan su suna waje, irinsu ko basu son mazan,ko kuma suna da wani da suke so Allah bai ƙaddara auren su ba ,don haka sai su rinƙa fita wajen su suna haɗuwa.

Mun tambaye ta aka ‘yammata sai ta ce..

Su kuma ‘yan mata maganar gaskiya,rayuwar ƙarya suke sanyawa kansu, a dole sai anji daɗi ko duk abinda ƙawa ta yi sai an yi.

Akwai kuma waɗanda samari ke hure masu kunne su yaudare su su ɓata su,daga baya su gudu su barsu,to kasancewar sun saba ,kuma basu samu mijin aure ba, sai su gaza tsare kansu,su rinƙa bin maza.

Duk dai idan aka zagaya,wannan halayyar,tana da nasaba ne,da kwaɗai, matsi na rayuwa, rashin tarbiya da kuma buƙata.

Da muka tambaye ta shawara da jan hankali ga mata.  Ga abin da ta ce..

Mata ya kamata su san kansu, su yi ƙoƙarin tsare mutuncin kansu da iyalin su,su nemi sana’a da zasu riƙe kansu,su guji shiga duk wani wajen da za’a kalle su matsayin marasa mutunci, sannan su fiddà ma zuciyar su kwaɗayi da son abin duniya da ƙarya, saboda duk waɗannan abubuwan ne ke sanyawa mace taji zata iya yin komi don ta samu kuɗin da zata yi hidimomin ta.

A ko wane irin yanayi kika samu kanki, ki yi imani da Allah, ki yarda da kanki, ki ɗauka kina cikin jarabawa ne ,sai kiyi addu’a da fatan Allah ya baki ikon cinye wannan jarabawa.

Ki sani babu abinda ya kai mutuncinki muhimmanci a gareki,don haka kiyi ƙoƙari ki tsare ma kanki kima da mutunci a idanuwan mutane,kuma kiji tsoro Allah!
Tabbas babu jarabawar data kai rashin miji a wajen ‘ya mace.
Allah ya jiɓinci lamarin duk wata mace da Allah ya jarabeta da rashin miji,ta hanyar rabuwa ko mutuwa.Allah ya bamu mafita baki ɗaya.

Leave a Reply