Albishirin Atiku ga Gombawa: Na yi alƙawarin farfaɗo da dam ɗin Daɗin Kowa, samar da lantarki, noman rani da titina

0
207
Dandazon mahalarta taron PDP a Gombe

 

Daga wakilinmu

A ci gaba da yaƙin neman zaɓen da PDP ke yi, ɗan takarar shugabancin ƙasa Atiku Abubakar ya yi wa Gombawa alƙawarin farfaɗo da Madatsar Ruwan Daɗin Kowa domin riƙa samar da wutar lantarki ga ƙasa, idan har aka zaɓe shi a 2023.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar dai ya yi wannan alƙawari ne lokacin da Rundunar Yaƙin PDP ta dira Gombe domin ci gaba da kamfen ɗin sa. Kuma ya yi alƙawarin gina dukkan titinan da su ka haɗe Jihar Gombe da Adamawaz Barno, Yobe da Bauchi.

Atiku ya ce ya tabbatar idan aka gina titinan waɗanda sun daɗe da lalacewa, harkokin kasuwanci da cinikayya a tsakanin jihohin biyar za su ƙara bunƙasa sosai.

“Mu na kuma ƙara jaddada cewa Daɗin Kowa Dam wanda dama tun asali PDP ce ta gina shi domin samar da wuta da noman rani, to idan mu ka ci zaɓe za mu sake farfaɗo da shi domin bunƙasa lantarki da noman ranin.

“Kuma za mu tabbatar cewa mun gina dukkan titinan da su ka haɗa Gombe, Barno, Bauchi, Yobe da Adamawa, domin inganta harkokin cinikayya,” inji Atiku.

Wazirin Adamawa, wanda ɗan asalin Jihar Adamawa ne, ya kwatanta kan sa da Firai Minista Abubakar Tafawa.

“Da yawa daga cikin ku ba a haife ku lokacin mulkin Abubakar Tafawa Ɓalewa ba. To a yau ga dama ta same ku ta sake samun wani Tafawa Ɓalewa ɗin idan ku ka zaɓe ni.”

Shugaban Kamfen ɗin Shugaban Ƙasa na PDP, kuma Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, ya ce idan PDP ta yi nasara a 2023, tattalin arzikin ƙasa zai bunƙasa, sannan darajar naira ita za ta farfaɗo.

Leave a Reply