An bayyana shirin sauraron ra’a yoyin jama’a kan batun ilmin bai ɗaya -Shugaban majalisar dattawa

0
134

 

Shugaban majalisar dattawa ya sanar da shirin sauraren ra’ayoyin jama’a kan batun ƙudurin samar da hukumar tsara ilimin bai-ɗaya.

 

A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne, shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya ayyana batun fara shirin sauraren ra’ayoyin jama’a dangane da batun farfaɗo da hukumar tsarawa da gudanar da ilimi ta ƙasa (NEIPA) a garin Ondo da ke jahar Ondo.

A shekarar 1992 aka fara kafa hukumar ƙarƙashin ma’aikatar ilimi ta ƙasa tare da haɗin guiwar hukumar duniya (UNESCO/IIEP) a matsayin kwalejin horar da ma’aikata na hukumomin Najeriya da kuma wasu ƙananan ɓangarorin Afirka ta yamma.

Yayin da yake zantar da manema labarai shugaban majalisar ya bayyana cewa, “wannan dama ce a gare mu da za mu tabbatar hukumar ta yi aiki tuƙuru kuma da gogewa.”

“Wannan wata dama ce da za ta sa mu sakin abin a buɗe, ba tare taƙaicewa tattaunawa a dokance ba, domin manufar ita ce hukamar ta samu damar yin aikin da ya dace.”

“Fatanmu da addu’armu sakamakon wannan jin ra’ayoyin da aka fara yau, ya zama wata dama ce da sanatoci za su iya amfani da ita domin yanke hukuncin da zai ciyar da hukumar gaba, ya sa kuma ta yi ake da ƙwarewa.”

“Ina kuma tabbatar muku da cewa, bayan zartar da wannan ƙuduri, za ku samu cikakken goyon baya domin sauke nauyin da aka ɗora muku a yadda ya dace.”

A jawabinsa na maraba shugaban kwamitin ilimi daga tushe wato sanata Ibrahim Gaidam ya bayyana cewa, hukumar tsarawa da gudanar da ilimin bai-ɗaya ta ƙasa wadda aka ƙirƙira a bana (2022), an samar da ita ne don ƙarfafar wadda ake da ita a baya.

Gaidam ya ƙara da cewa ita hukamar da aka kafa 1992 wadda ke da manufofi guda uku domin ciyar da tsare-tsaren da gudanar da ilimi gaba bisa gogewa.

“Manufar wannan shiri ita ce, don masu ruwa da tsaki da ma ragowar al’umma su samu damar gabatar da ra’ayoyinsu kafin sanatoci su kai ga yanke hukuncin tabbatar wannan tsari ko watsi da shi.”

Shi ma a nasa jawabin yayin da ake tsaka da gabatar da shirin sauraren ra’ayoyin jama’a, sanata Ayo Akinyelure cewa ya yi, “Abu ba daɗi duk cewar hukumar ta shafe tsawon shekaru, amma ba ta samu tanade-tanade da dakokin da za su sanya ta gabatar da ayyukanta da kuma dokokin da aka ɗora mata yadda ya kamata ba.

Dalilin wannan shiri shi ne, jin ra’ayoyin masu ruwa da tsaki domin samar da wasu dokokin da za su jagoracin wannan hukuma ta kai gaci.”

Leave a Reply