AN BINNE TSOHON SHUGABAN YANSANDA TAFA BALOGUN A GARINSU

0
69

 

An yi jana’izar tsohon Sufeto-Janar na ‘Yansanda  Mista Tafa Balogun, a gidansa na Ila-Orangun, Osun, ranar Asabar.

An naɗa Balogun a matsayin Sufeto-Janar na ‘Yansandan Najeriya na 21 a ranar 6 ga Maris, 2002. Ya bar ofishin a shekarar2005.

 

Ya rasu a Legas ranar Alhamis, kwana huɗu ya cika shekaru 75 da haihuwa.

An gudanar da Sallar Jana’izar kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada a filin Sallar Idi na tsakiyar Ila-Orangun.

Babban Limamin Ila-Orangun, Dr Abdulhammed Salahudeen, shi ne ya jagoranci sallar jana’izar inda ya yi wa’azin buƙatar ‘yan Adam su yi aikin alheri saboda babu makawa  ga mutuwa.

Tsohon Sufeto-Janar na ‘Yansandan Najeriya, Solomon Arase, wanda ya zanta da manema labarai a wajen jana’izar, ya bayyana Balogun a matsayin ɗaya daga cikin mafi girman ‘Yan sandan da Najeriya ta taɓa samar wa.

Arase ya bayyana IG-P mai barin gado a matsayin jagora kuma Uba wanda ya yi tasiri ga Jami’an ‘Yansanda da yawa a hankali.

Ya ce: “Shi jajirtacce ne abin koyi mai aiki, da hankali ga asali; Jami’in duk da mutuwarsa zai kasance abin koyi.

“Ya kasance kamar babban Uba idan ana maganar aikin ‘Yansanda. Koyaushe kuna iya zuwa wurinsa don neman shawara kuma za mu yi kewarsa a kan hakan.’’

NAN ta ruwaito cewa kwamishinan ‘Yansandan Jihar Osun Mista Olawale Olokode ne ya wakilci babban sufeton ‘Yansanda  na yanzu, Usman Alkali Baba a wajen jana’izar.

Babban Sakataren yaɗa labarai na Gwamna Gboyega Oyetola na Osun, Mista Ismail Omipidan, da Kwamishinan kuɗi na Osun, Bola Oyebamiji, duk sun wakilci Gwamnatin Jihar a wajen Jana’izar, wanda ya samu halartar Jami’an ‘yansanda.

Leave a Reply