DAGA ABU USAIMIN.
A ranar Litinin ɗin ta gabata ne, gwamnatin tarayya ta sanar da sake buɗe hanyar sufuri ta layin dogo daga Abuja zuwa Kaduna.
Ministan sufuri malam Mu’azu Sambo ne ya bayyana hakan yayin gabatar da ƙudurorin da shugaban ƙasa ya cimma tsakanin 2015 zuwa 2022 a ma’aikatar sufuri da ke Abuja.
Hukumar yaɗa labari ta ƙasa wato (NAN) ce ta rawaito dakatar da sufuri ta layin dogo, tun bayan harin da ‘yan ta da ƙayar baya suka kai wa wani jirgin ƙasa mai ɗauke da fasinjoji a ranar 28 ga watan Maris na wannan shekarar. An yi garkuwa da dukkan fasinjojin tare da lalata jiragen ƙasa a kan titin dogon.
A watan Oktoba ne gwamnati tarayya ta tseratar da ragowar mutum 23 ukun da aka yi garkuwa da su. Kuma ta shelanta cewa za a dawo da sufuri bayan tabbacin ɗaukar matakan tsaro.
A cewar ministan “Harin Abuja zuwa Kaduna abin takaici ne ƙwarai. Kuma in sha Allah ba za a sake maimaita irinsa ba. Ba wai iya addu’a muka yi ba. A’a mu ɗauki matakan kariya. Sannan kamar yadda ka faɗa, mun ɗauki izina, kuma za mu yi amfani da darasin da muka ɗauka.”
“Waɗanne irin darusa muka ɗauka? Kyautata tsaro da sanya idanu a tsawon awanni 24 na kowace rana, a kuma duk kwanakin mako tsawon watanni 12 na shekara.
Minista zai zauna a ofishinsa yana kallon yadda abubuwa ke gudana. Haka shugaban ƙasa da kansa, haka nan darakta na jami’an tsaro jaha (State Security Service)shi ma, da ma sauran jami’an tsaro.
Waɗannan su ne matakan da muka ɗauka. Ba za mu sake yarda wani ya yi mana zagon ƙasa ba. A wannan watan na Nuwamba harkoki za su dawo, ina faɗa muku ne domin masu rahoton jaha su shaida, babu abin da za a cigaba har sai kowane daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su ya koma cikin iyalinsa lafiya ƙalau.
Allah ya sanya abubuwa sun tafi yadda ya kamata bisa ƙoƙarin hukumomin tsaro da kuma jagorancin mai girma shugaban ƙasa. Yanzu komai ya zama tarihi, babu wani wanda ya samu rauni daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su. Muna gode wa Allah.