Daga Wakilinmu
Jami’an ‘yansanda sun kama wani matashi mai shekaru 24 mai suna Clement Joseph wanda yake iƙirarin shi likitane. Ya kuma yi amfani da hakan wurin yi wa ‘yan mata huɗu ciki, tare da zubar wa ɗayar cikisu.
Daily post ta rawaito cewar an kama Joseph ne a ranar asabar 6 ga watan Nuwamba, a Chanchaga da ke jahar Minna.
Jami’i mai kula da hulɗa da jama’a na hukumar ‘yan sandan jahar Neja wato DSP Abiodun Wasiu ya ce ana zargin matashin ne da manyan laifuka guda uku; sojan gona, zamba, da kuma zubar da ciki.
Bayan batun sojan gona da Joseph harwayau ya karɓi kuɗaɗen wani bawan Allah da sunan yin kasuwanci ta yanar gizo mai suna Zuga Coins International business. Kuɗaɗen sun kai kimanin 280,000.
Abiodun ya bayyana cewa bayan da aka tsananta bincike ne, wanda ake zargin ya tabbatar alaƙantuwa da ‘yan mata guda huɗun da ya lalata.
A cewarsa, “wanda ake zargin ya gama da ɗaya wadda ta ke kan guiwa a yanzu, sai kuma ɗayar da ya zubar mata da ciki.”
A yanzu haka ana cigaba da bincike.