An kama mutum ukun da suka yi garkuwa da yaro ɗan shekara 6 sannan kuma suka kashe shi

0
150

 

Gaga Abu Usaimin

‘Yan sandan jahar Zamfara sun tabbatar da cafke mutum ukun da suka yi garkuwa da wani yaro mai shekaru 6, sannan kuma suka kashe shi bayan sun karɓi kuɗin fansa kimanin Naira miliyan 2.5.

Mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan jahar wato Muhammad Shehu, ya bayyana waɗanda ake zargin Kabiru Idi, Ɗan hauwa Kalla da kuma Majami Iliya sun yi garkuwa da yaro ɗan shekara 6 mai suna Laminu Sani a garin Bulunku da ke birnin Gusau, sannan kuma suka buƙaci kuɗin fansa.

Bayan karɓar kuɗin fansar, sai suka ƙi sakin yaron, daga baya kuma aka gano gawarsa an jefar da ita.

“A ranar 3 ga watan Nuwamba ne jami’anmu ɓangaren kwantar da tarzoma suka kama waɗanda ake zargin sun yi garkuwa da kisan Laminu Sani ɗan shekara 6 a Bulunku da ke Gusau.” A cewar Shehu.

“An cafke su ne bayan da wani bawan Allah mai suna Sani Garba ya shigar da ƙara a kan cewa Kabir Idi da ke ƙauyen ‘Yarkatsina ya kama hayar ɗaki a gidansa kuma ya zauna tsawon wata uku.

A lokacin da yake zaune a gidan ne, ya haɗa baki da abokan harkar tasa suka kama ɗan malam Sani mai suna Laminu, kuma suka buƙaci kuɗi har miliyan 2.5”

“Bayan an damƙa musu kuɗin da suka buƙata ne, aka gano cewar tuni ma sun kashe yaron. A yayin da ake gudanar da bincike, waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu. Da kuma yadda suka yi garkuwa da yaron.”

Shehu ya tabbatar za a miƙa su zuwa kotu don tabbatar da adalci.

Leave a Reply