AN KAMA WANI MAHAIFI DA AKE ZARGIN YA JEFE YAYANSA A ADMAWA

0
68

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta kama wani mutum da ake zargi ya jefe ‘ya’yansa biyu da kuma dukan su da sanda har sai da suka mutu a Jihar Adamawa da ke arewacin ƙasar.

Ana zargin mutumin mai suna Elisha Tari mai shekara 25 da yi wa ‘ya’yan nasa duka, mai shekara biyu da mai uku, bayan sun rabu da mahaifiyarsu wata biyu da suka wuce.
A cewar sanarwar da rundunar ta fitar ranar Asabar, binciken farko-farko da aka gudanar sun nuna cewa mutumin mazaunin Ƙaramar Hukumar Michika, ya kashe yaran ne bayan sun samu saɓani da mahaifiyarsu.

Ana zargin ya yi amfani da sanda kuma ya yi ta dukan su a ka. Hotunan da rundunar ta wallafa sun nuna yaran kwance, kansu duk ƙura da kuma jini.

An kama wanda ake zargin ne yayin da yake yunƙurin tsallakawa zuwa ƙasar Kamaru mai maƙwabtaka, a cewar ‘yan sanda, kuma yanzu haka ana ci gaba da bincike don gano ainahin abin da ya faru.

Leave a Reply