Shuguban majalisar dokoki ta ƙasa Femi Gbajabiamila ya roƙi ‘yanƙungiyar ASUU da su kwantar da hankalinsu bisa ga abin da ya faru na biyansu rabin albashinsu.
A bayanin da Kakakin majalisar ya gabatar a ranar Litinin a garin Abuja, ya tabbatar yunƙurin nemon bakin zaren wannan ƙorafi.
A cewar shugaba Muhammad Buhari yana ƙoƙarin share musu hawayensu sakamakon kokensu na baya-baya nan. “A lokacin da ASUU ta janye matakin da ta ɗauka (yajin aiki) a makwanni uku da suka gabata, wannan ya nuna jami’o’in gwamnati za su dawo bakin aikinsu ka’in da na’in.”
A cewarsa “Majalisar tarayya na ƙoƙarin shawo kan matsalolin da suka janyo tsunduma cikin yajin aikin.
Kuma a yanzu haka majalisa tana aiki a kan tsarin kasafin kuɗi na shekarar 2023. Kuma wannan zai yi malaman jami’o’in tanadi abubuwa na walwala da jindaɗi na kimanin biliyan 170. Hallau tsarin ya yi tanadin ƙarin biliyan 300 uku domin sabuntawa da kuma gyaran gine-gine da ke jami’o’in.
Sannan majalisar ta yi kira ga akauta janar na ƙasa (AGF) da kuma su malaman domin su karɓi sabon tsarin biyan albashi na (UTAS) da kuma (IPPS). Tsarin ya samu bibiya da kula ƙarƙashin jagorancin kwamitin ilimi na manyan makarantu Aminu Sulaiman.
Tsarin ba iya wajabta biyan albashin malamai ya mayar doka ba, hallau ya sharɗanta gwamnatin kula da duk wasu ayyukan da ake aiwatarwa da kuma kariya daga ibtila’an da ka iya faruwa.
Duk wani matakin da biyan albashin na malamai an ɗauka, bisa ga yanayi maikyau daga shugaban ƙasa. Shugaba Buhari ya ɗauki matakin daƙile sake faruwar hakan. Tsarin ilimin manyan makarantu da majalisa ta yi, ta hanyar jin ra’ayoyin al’ummma, shi ne za ɗabbaƙa.