Atiku ya yi alƙawarin kashe dala biliyan 10 don samar da ayyuka da inganta rayuwar mata da matasa

0
83
Ɗan takara Alhaji Atiku Abubakar tare da jiga-jigai a Jam 'iyya

 

Ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin cewa idan ya yi nasara a zaɓen 2023, gwamnatin sa za ta ware dala biliyan 10 don bunƙasa rayuwar mata, samar da ayyuka, ƙanana da matsakaitan masana’antu da sana’o’i.

Ya ce waɗannan zunzurutun kuɗaɗen za su kuma yi amfani wajen tallafa wa mata da matasa kaiwa ga matakan nasarar da su ke ta hanƙoron ganin sun cimma burin kaiwa.

Wani sashe na taron

Atiku ya sha wannan alwashin a Ilorin, babban birnin Jihar Kwara, lokacin da ya je yaƙin neman zaɓe a can.

Atiku wanda ya yi mataimakin shugaban ƙasa daga 1999 zuwa 2007, ya ɗora laifin matsalar tsaro a kan gwamnatin APC.

Ya ce gwamnatin Buhari ta gaza kuma ta yaudari ‘yan Najeriya a fannin tsaro da ayyukan gina ƙasa.

Dandazon magoya baya

Da ya ke taya Jihar Kwara nuna damuwar sa kan matsalolin jihar, Atiku ya nuna takaicin duk da jihar Kwara ce mahaɗar Arewa da Kudu, amma ba ta da hanyoyi masu kyau.

Shi kuwa Shugaban PDP Iyorchia Ayu,

Dandazon  mata

cewa ya yi “jam’iyyar PDP babban gida ne wanda kawunan dukkan iyalan gidan a haɗe su ke. Mu na kan hanyar kaiwa ga nasara.

“PDP za ta dawo ta ceci Nijeriya, ta maida ta kan turbar bunƙasa da ceton kowane iyali.”wa

“Kada

ku bari wasu su yaudare ku, yunwar da ta yi mana katutu a yanzu ta nunka wadda mu ka sha a 2015. Kowa ya fito da katin zaɓen sa ku zaɓi PDP, ku zaɓi ɗan takarar ta Atiku Abubakar a zaɓen 2023,” inji Ayu.

Leave a Reply