Buhari: Don Allah Ka Dakatar Da Gwamnan CBN Kan Badakalar $171 biliyan

0
65
Hon Gudaji Kazaure

 

Daga Dakta Aliyu U. Tilde

Shawarar da ɗan Majalisar Tarayya, Alhaji Gudaji Kazaure, ya bayar na dakatar da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), tana da kyau sosai kuma tana bisa ƙa’ida. Kai, ma iya cewa ma ta zama babbar buƙatar ƙasa a yanzu.

Idan ba a ɗaga kaza daga makwancinta ba, ba za a san me fukafukanta suka ɓoye ba. Don haka ƙa’ida ce mai kyau idan za a yi bincike mai zurfi musamman idan wanda yake shugabantar wurin yana nuna tirjiya da kokarin danne gaskiya, to a dakatar da shi.

Shugaba Buhari ya sa Hon. Kazaure aikin bincike a CBN saboda wani labari mai tada hankali da ya ji. Ya ce kuma Hon. ya ba shi bayanin abinda ya gano kai tsaye ba tare da ya biya ta kan wani jami’i ba.

Yanzu kwamitin Hon. Kazaure ya gano wata badaƙala ta $171 biliyan wacce ba a taɓa yin irinta ba a Nijeriya. Hon. ya ce kuɗi ne wanda aka ce na masu zuba hannun jari ne amma kuma majahulai. Kwamitinsa ya yanke cewa talakawa ake ta tatsa ta hanyar charges har aka tara su aka yi kwana da su.

Hon ya tattara bayanai ya doshi Shugaban Ƙasa da su amma dogarin Shugaban Ƙasa da aka haɗa shi da shi don iso wajensa ya hana ya gan shi. Jama’a, akwai rina a kaba!

Ya kamata ‘yan Nijeriya su ba wannan magana muhimmanci sosai. $171 billion a zamanin yunwa da rugujewar tattalin arziki ba wasa ba ne. Kuma mun ci sa’a a zamanin Buhari ne. Don haka, dole a matsa a yi abinda ya dace. Kar mu zame kamar kazar da ta kwana a kan dami…

Muna ƙarfafa wa Shugaban Ƙasa gwiwa a kan ya buɗe ƙofarsa, ya gayyaci Hon. Kazaure, ya gan shi, ido da ido, kuma ya miƙa masa bayanan abinda ya gano, yadun bi yadin. Abin da ɗaure kai a ce wasu na jikin Shugaba Buhari za su hana Hon. isa wajensa har sai ya fito bainar jama’a yana roƙo.

Masu bai wa Shugaban Ƙasa shawara da na jikinsa ya zama dole su ba shi shawarar tunkarar wannan ƙazamin lamari da gaske. Magana dai ta fito, fiye da ta $16 biliyan na Obasanjo a Mambila, ko ta $20 biliyan na Diezani da Jonathan. Ba wanda zai so mulkinsa ya ƙare da irin wannan badaƙalar a kwance. Dakatar da Gwamnan CBN da kammala binciken da gaggawa ya zama dole.

Shi kuma Hon. Gudaji Kazaure ya san cewa ya burge mu. Ya tabbata ɗan mu ne na asali mara tsoro, mai tsayawa a kan gaskiya da riƙon amanar da aka ba shi. Allah saka masa da alheri, ya kiyaye mana shi.

Dr. Aliyu U. Tilde ɗan siyasa ne mazaunin Bauchi

Leave a Reply