BUKIN SALLAR TAKUTAHA

0
40

 

Tattarawa Kabiru Yusuf Fagge (Anka)

Akwai sabani a kan maanar kalmar “Takutaha” ; wadansu su ce maanarta Allah ya maimaita mana. Wadansu kuwa sun ce wai ita wannan kalma sunan Maaiki ne. A wata fadar kuma an ce ita wannan kalma an samo ta daga maganar Shaihu Usmanu Danfodiyo. Wai wata rana ne almajiransa suka je bara a wannan rana ta murnar zagayowar ranar haihuwar annabi Muhammadu (S.A.W.) da suka dawo sai suka kawo masa abin da suka samo a wajen barar, amma a maimakon ya dauki wani abu daga ciki, sai ya ce, “Ai wannan taku ta” watu yana nufin “taku ce.” To daga wannan magana “taku ta” aka sami kalmar “Takutaha” . Amma duk wadannan maganganu ba su da wani tushe mai kwari, don kuwa jin su na yi kawai a bakin wasu mutane.

Bukin Sallar Takutaha yana daya daga cikin bukukuwan addini da ake yin sa a Birnin Kano. Malaman tarihi sun ce an fara wannan buki a Kano tun zamanin Sarkin Kano Abubakar Kada A.H 973-980/1565-1573AD wajen shekaru dari hudu da suka wuce ke nan. Ana yin bukin sallar Takutaha ranar sha tara ga watan Rabiul Awwal, watau watan da aka haifi Annabi Muhammadu (S.A.W.) sabanin ‘sallar Gane’ ta Daura wadda ake yin ta ranar sha biyu ga watan, watau daidai ranar da aka haifi Annabin ke nan. Su mutanen Kano sun dauki nasu buki ya zama ranar suna, watau bayan kwana bakwai da yin haihuwar. Watau a wurin mutanen Kano taron bukin Takutaha taro ne da ake yin sa don tunawa da zagayowar ranar da aka yi sunan Annabi Muhammadu (S.A.W), saboda haka ya zama ran sha tara ga wata. An haifi Annabi ranar sha biyu ga wata, idan Ranar ta kewayo ya zama ranar goma sha tara ke nan. Yin bukin Takutaha ranar suna ya dace da al’adar Hausawa ne ta wajen yin shagulgulan buki ran sunan jariri, ba ranar haihuwarsa ba.

Shi wannan buki bai shafi saraki ba, don haka ba a yi masa wani hawan dawaki. A ranar bukin ba a gayyatar kowa don ya zo kallo ko ya hau doki. Kai a takaice dai ko mai unguwa ba lallai ne ya je wurin bukin ba. Ana yin wannan buki a unguwar Madabo ne can arewa da kasuwar Kurmi kusa da dutsen Dala. Kuma ana yin bukin ne a tsakanin gidan Babban Malami na Madabo da masallacin Madabo.

Idan ana gobe za a yi bukin a bisa al’ada Sarkin Kano yakan aika wa Babbanm Malami da sa wanda za a yanka a yi sadaka, kuma a ran nan da yamma jama’ar gidan Babban Malami da mutanen unguwar Madabo za su shirya saboda taron bukin a shasshare wuraren da suka kamata, a yi kuma shimfidu a wuraren da suka kamata. Wadansu masu gida da dama a cikin birnin Kano musamman unguwoyin da suka kewaye bakin kasuwa sukan yi shirin abinci kamar irin na bukin sallar Idi. Wadansu ma har sukan yanka dabbobi don shirin abincin Takutaha. Irin wannan abinci da safe akan aika da shi Madabo gidan Babban Malami don a yi sadaka. Wdansu kuma sukan ci tare da iyalansu ne, kuma su raba wa makwabta. Haka kuma almajirai sukan kwana suna rubutu suna wankewa a cikin kwatanniya, don tanadin rubutun da za a bai wa jamaa ranar sallar.

A ranar Takutaha da safe sai jamaa, musamman mata tsofaffi da yara su ci ado su kama hanyar zuwa Madabo. Idan za a tafi wadansu mata sukan yi guzurin auduga ko kwalli, ko kuratandu don su kai wa Babban Malami ya yi musu tofi a ciki don neman albarka. A can Madabon kuma wajen misalin karfe tara na safe sai malamai su shiga Masallacin Madabo su fara karatu. Sukan karanta wakokin yabon Annabi, musamman waken Ishiriniya. A lokacin da suke kwarantunsu a masallaci shi kuwa Babban Malami yana zaune a soronsa tare da sauran malamai mukarrabansa kowa ya ci ado da manya-manyan riguna da rawuna. Shi kuwa Babban Malamin har da alkyabba. Mutane maza da mata tsofaffi za su yi ta kokarin shiga soron Babban Malami don ya yi musu addu’a. A lokacin ne matan sukan ba da audugarsu ko kwalli, ko kuratandu don Babban Malami ya yi musu addu’a a ciki. Wadansu mutane sukan kawo sadaka a lokacin da ake wannan zama. Kafin sha biyun rana mutane sun cika Madabo fal. Tsakanin gidan Malamin da masallacin yakan cushe da kyar ake samun hanyar wucewa. Wasu na kokarin zuwa Masallacin don su ji karatu, wasu kuma na kokarin zuwa gidan Malamin. Masallacin yakan cika makil, mutane har kan katanga. A lokacin da ake wannan buki kuma wasu samari za su yi ta zagawa da rubutun sha fal kwarya suna diba suna ba mutane, suna cewa, A sha, a shafa, sadaka sai an niyya. Wadansu kuma suna zagawa da allunan sauka masu zayyana a ciki suna cewa, A shafa, sadaka sai an niyya. A lokacin kuma za ka ga wadansu samari suna kokarin debo ruwan masallacin da kasar suna bai wa mata da yara ana ba su sadaka, wai don neman albarka. A tsakanin masallacin da gidan malamin kuma akan sami wani saurayi ya sha nadi ga samari a gabansa, ana ta rubutu, ana wankewa a kwatanniya ana bai wa jama’a suna sha. Irin wadannan samari sukan ce wai mai nadin nan jikan Babban Malami ne. Sai mata su yi ta zuwa wurinsa suna ba shi sadaka yana yi musu addu’a ko tofi a cikin auduga, ko kwalli. Sau da yawa akan sami ganyen baure a gabansa. Wai wannan ganyen bauren gonar Babban Malami ne. Jama’a za su yi ta ba da sadaka a ba su ganyen don neman albarka. Haka dai abin zai ci gaba har kusan Azahar.
Idan Azahar ta kusa sai malaman da suke karatu a masallacin su aiko a gaya wa Babban Malami sun hada karatun. Daga nan sai Babban Malami tare da jama’a da suke tare da shi ya fito ya kama hanyar masallacin. A kan hanya jama’a suna ta kokarin su gan shi. Idan ya isa masallacin, sai a raba abin da aka samu na sadaka. Daga nan sai ya yi musu addu’a. Da zarar an gama addu’a sai jamaa su fito daga masallacin a raka malamin zuwa gidansa. Idan ya isa gida, sai ya tsaya a kofar gidan ya yi addu’a kowa ya shafa. Shi ke nan sai ya shiga gida buki kuma ya kare, sai badi in Allah ya kai rai.
Idan buki ya tashi daga Madabo kuma sai jama’a su kasu uku. Dattijai maza da mata da suka halarci bukin yawanci sai su kama hanya su koma gidajensu. Su kuwa yara sai su tafi su hau kan Dutsen Dala. A can ma yara za su sake yin wani bukin. A kan Dalar za a sami masu neman sadaka da yawa. Wasu mutanen kuma za su sami wuri su kame, suna jan carbi ba sa magana da kowa, wai su waliyyai ne. Mutanen da suke zaune tare da shi, su za su yi magana da mutanen da suka ba shi sadaka. Wasu samarin har wani kogo sukan samu a kan Dutsen Dala su shiga ciki. Yara suna lekawa, suna kallo suna ba su sadaka. Yawanci yara sukan yi ta yawonsu a kan Dutsen Dala har bayan Azahar, sa’an nan su dawo gida, su shirya, su tafi barar Takutaha. Samari kuwa yawanci ana watsewa daga Madabo sai su bazu cikin gari suna barar Takutaha. Wadansu su fantsama cikin kasuwar Kurmi, wadansu kuwa su datse hanyoyin cikin gari suna tare matafiya suna yi musu barar Takutaha. Yara kuwa za su dinga shiga gidaje suna yin tasu Takutahar. A lokacin da ake yin wannan bara ta Takutaha a kan rera wake kamar haka:

Takutaha bara muke, takutaha sadaka.
Takutaha ta Annabi, takutaha sadaka.
Takutaha yau sallah, takutaha sadaka.
Takutaha mai gero, takutaha sadaka.
Takutaha mai dawa, takutaha sadaka.
Takutaha daga wannan, sai ta badi sadaka.
Sai ta badi, Allah ya kai mu badi sadaka.
Takutaha Allah karba, takutaha sadaka.

Haka yara da samari da yanmata za su cika gari gida-gida, lungu-lungu, hanya-hanya, suna yin wannan bara har faduwar rana. Daga nan kuma sai a daina. Ba za a kar ayi ba, sai badi in Allah ya kai mu irin wannan ranar.

Sallar Takutaha babbar rana ce a cikin garin Kano, don wannan rana takan zama kamar ranar hutu musamman ga yaran makarnatar allo da kuma yan kasuwa, wadanda yawanci ko mutum ya je kasuwar a wannan rana babu wani ciniki da zai samu sosai sai dai ya yi ta fama da yan Takutaha. A shekarun baya da suka wuce wannan rana har an sa ta a cikin ranekun hutun yan faramare saboda muhimmancin bukin a wurin yara. Wadansu suna ganin bukin da yara suke yi a kan Dutsen Dala ba zai rasa alaka da bautar gunkin Tsumburbura ba wadda jama’ar Kano suke yi tun kafin zuwan addinin Musulunci. Irin wadannan mutane suna ganin bayan da Musulunci ya zo ya hana wannan bauta, tasirinsa bai fita ba daga zuciyar mutane; don haka ne duk shekara yara sukan hau kan Dutsen Dala a wannan rana, kamar yadda mutanen Kano suke bukin shekara-shekara a kan Dutsen Dala don bautar Tsumburbura.

An tsakuro daga:
DANGANTAKAR ALADA DA ADDINI: TASIRIN MUSULUNCI KAN RAYUWAR HAUSAWA TA GARGAJIYA na Muhammadu Sani Ibrahim
Kundin Bincike Don Samun Digiri na Biyu (M.A.) a Sashin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano (Afrilu, 1982)

Leave a Reply