Labarai

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA ta cafke ɗaliba mai ciki da gurgu ɗauke da miyagun ƙwayoyi

 

 

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi watau NDLEA ta samu nasarar cafke ɗalibar makaranta, da mace mai cike tare da wani gurgu bisa laifin safarar miyagun ƙwayoyi.

Hukumar ta bayyana nasarar cafke ɗalibar mai suna Isoyo Ivaren Susan, mai shekaru 22, da matakin HND 1 a kwalejin fasaha ta tarayya dake Ilaro, Jihar Ogun da laifin safarar miyagun ƙwayoyi.

An cafke Susan ne a ranar asabar 15 ga watan Afrilun 2023, a daura da ƙofar shiga kwalejin da laifin safarar miyagun ƙwayoyi.

Hukumar ta samu nasarar ƙwato awon mil 1,100 na magungunan tari masu ɗauke da sinadarin codeine gami da giram 283 na sinadarin cannabis.

A wani labarin kuma, jamian hukumar sun samu nasarar damƙe wata mace mai ciki mai suna, Rabetu Abdulrasak, mai shekaru 24, da kuma wani gurgu da irin wancan laifin a cikin Agbede, Etsako West LGA, jihar Edo .

Jamian hukumar sun samu waɗanda ake zargi ɗauke da miyagun ƙwayoyi da aka haramta tu’ammali dasu, don haka hukumar tace tana cigaba da faɗaɗa bincike akansu kafin gabatar dasu a gaban kuliya.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button