Daga Kamal Aliyu Sabongida
ƘUNGIYAR Dattawan Arewa (Northern Elders Forum, NEF) ta bayyana kalaman da Gwamnan Jihar Binuwai, Mista Samuel Ortom, ya yi a matsayin ‘masu tsauri’, wanda a lokacin da ya ke yin Allah-wadai da kisan mutane 18 da aka yi a yankin karamar hukumar sa a ranar Juma’a da ta gabata ya ce ba zai ta
ba goyon bayan wani Bafulatani ya sake zama shugaban ƙasar Nijeriya ba.
Ortom ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke karbar bakuncin takwarorin sa na jihohin Ribas, Oyo, Abiya da Inugu a wajen wata liyafar cin abinci a Makurdi.
Ya ce: “Ku na so in zama bawa ga Bafulatani. Gara in mutu. Ana kashe mutane na, ku na so in yi shiru. Ba zan taba goyon bayan Bafulatani ya zama shugaban kasa ba. Idan kuma akwai wani wanda ya ke shirye ya yi aiki tare da ni don tabbatar da tsaron jama’a ta, zan yi aiki da shi.”
Sai dai Ƙungiyar Dattawan Arewa, a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labarai na ƙungiyar, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ta ce kalaman gwamnan kwata-kwata ba su dace da shugaba ba, musamman a daidai lokacin da ake siyasantar da matsalar rashin tsaro a kasar nan.
Ƙungiyar ta ce, “Mu ma, kamar sauran ‘yan Nijeriya, mun kalli bidiyon da Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom, ke magana a cikin yanayi da kuma yare da bai dace da shugaba ba.
“Ƙungiyar Dattawan Arewa ta ci gaba da yin Allah-wadai da yanayin ƙawanya da rashin tsaro da ‘yan Nijeriya su ka yi rayuwa a ƙarƙashin su a cikin ‘yan shekarun nan, musamman a Arewa ‘yan damfara Fulani sun yi fice a matsayin masu kisa da ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane.
“Ya kamata Gwamna Ortom ya cika rantsuwar da ya yi da kuma alƙawarin da ya yi na yin rayuwa a matsayin sa na shugaban al’ummar sa.
“Ya kamata ya guje wa sha’awar buga wasan kwaikwayo wanda, kamar sauran ‘yan Nijeriya, ke da burin samun sauƙi da kuma kawo karshen kashe-kashen da ke tayar da juna da kuma kai su ga rikice-rikice marasa iyaka.”