FCTA na yunƙurin rufe kasuwar Area l saboda wasu ayyuka da ka iya zama barazana ga lafiya.

0
151

 

Babban birnin tarayya na yunƙurin rufe manya shaguna da kasuwar Area I bisa la’akari da wasu ayyukan da ke barazana ga ingantacciyar lafiya.

Kwa’odinatan da ke kula da ɓangaren gudanarwa na ƙwaryar birnin tarayya Abuja (AMMC) Malam Umar Shu’aib ya yi wannan gargaɗi bayan da ya kai ziyara shi da wasu
daga cikin jami’a biyo ƙorafe-ƙorafe da kuma kiraye-kirayen da ake a kan hakan.

Malam Shu’aib ya bayyana cewa duk da kasantuwar babban shago na farko a garin, akwai buƙatar ya kai matakin ya kamata.

An bunƙasa kasuwar ne domin abubuwa mabambanta, amma ‘yankasuwar sun ruguza duk wani tsari da aka yi.

Hukuma za ta ɗauki matakin da ya ce daga zarar kwamitin da ta ɗora alhakin bincike ya gabatar da sakamako.

Kwamitin ya ƙunshi hukumomin tsare-tsare, sashe-sashe da sakatariyoyin birnin tarayya. Daga zarar kwamatin ya kammala, za mu yi garambawul. Wasu gine-ginen za a yi musu kwaskwarima, wasu kuma a sauya musu muhalli.” A cewarsa.

Ya kuma nuna rashin jindaɗinsa bisa ga yadda wani yanki na kasuwar yake a cunkushe ba tare da lura da hanyoyin kiwon lafiya ko tsaftar muhalli ba.

“Mun kasance a kasuwar ne saboda yin bincike a kan wasu bayanai da kuma ƙorafe-ƙorafe da aka gabatar mana.

Kusan ko’ina na kasuwar a cunkushe yake, duk da cewar akwai wuraren da aka tanada saboda tafiyar ƙafa, da kuma ajiye abubuwan hawa. Don dole wannan tsari mu ga an aiwatar da shi. Dole za mu dawo da batun tsafta ta hanyar kau da duk abin da ba yi shi bisa ƙa’ida ba. Wuraren da za a rushe, za mu rushe, wasu kuma mu sauya musu wuri. Wannan kasuwa ce ta duniya ba ta ƙasa ba, don haka dole ta kai matakin da ya dace da ita.”

Leave a Reply