Game Da Mu

Fasihiya jarida ce wadda aka kafa domin yaɗa labaran ƙasa da na duniya tare da faɗakarwa da nishaɗantarwa. Alƙiblar mu ita ce kawo rahotanni da ra’ayoyi kan zamantakewa baki ɗaya, musamman a ɓangarorin siyasa, tattalin arziki, addini, harkar ilimi, kiwon lafiya, adabi, sana’o’i, da sauran su.

Burin mu shi ne mu taimaka da basirar da Allah ya ba mu wajen ƙara wa masu karatun mu masaniya game da abin da ke faruwa a rayuwar mu ta yau da kullum. Ta wannan hanyar mu ke fatan jama’ar mu za su samu ƙarin wayewa domin yaƙar jahilci, rashin sani, zaman kashe wando, cin hanci da rashawa da sauran matsaloli.

Mu na da burin ganin iyalai sun kyautata rayuwar su wajen kula da rayuwar mata, ƙananan yara, naƙasassu da marasa galihu.

Mu na fatan za a ba mu goyon baya domin cimma wannan manufa. Kuma mu na fatan za a tuntuɓe mu a ko yaushe domin ba mu shawara ko gyara saboda mu kyautata aikin mu.