GIMBIYA ANNE CE TA YI WA GAWAR SARAUNIYA RAKIYA ZUWA EDINBURGH

0
87
Gimbiya Anne tare da mijinta

Gimbiya Anne tare da mijinta wanda babban hafsan sojin ruwan ƙasar ne wato Vice-Admiral Sir Tim Laurence sun yi wa gawar sarauniyar rakiya zuwa Edinburgh daga fadarta da ke Balmoral a yankin Scotland.

Bayan kwashe sa’o’i shida ana wannan doguwar tafiya a mota, a yanzu gawar ta isa fadar Sarauniyar ta Holyroodhouse, wadda ke birnin Edinburgh, kuma a cikin makon da za mu shiga ne za a wuce da ita zuwa birnin Landon domin yi mata jana’izar kasa.

A yayin wannan doguwar tafiya da aka bi ta garuruwa manya da ƙanana da kauyuka, sun sha tarba da nuna girmamawa daga duk jama’ar da aka bi ta garuruwansu.

Leave a Reply