GUZURIN ƘAUNA

0
181

 

Soyayya mai karatu,
Gona ce sai da noma,
Asa taki da maimai,
Sai ƙauna tai yabanya.

Mai zaton cewa a kwance,
Za a so shi yana da wauta,
Zuciyar mai sonka tabbas,
Gona ce bibiye ta.

Kasassabe duk ƙirare,
Haki in zaka nome,
Ba kasala ba gazawa,
Za kai nasara ka lura.

Kulawa ce fatanya,
Haƙuri taki na ƙauna,
Yafiya kyauta mutunci,
Su ke sawa a soka.

Kwaɗayi mita butulci,
Su ke sawa a ƙika,
Guzuri jari na ƙauna,
Kyautatawa bar musawa.

© Khalid Imam
7/8/2022
3:25nr.

Leave a Reply