GWAMNA BABAGANA UMARU ZULUM YA AMINCE DA TALLAFIN NAIRA MILIYAN 19,3 GA ƊALIBAI MARASA GALIHU A FANNIN SHARI”A

0
165

 

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya amince da fitar da Naira miliyan 19.3 domin biyan alawus-alawus na tallafin karatu ga dalibai marasa galihu 59 da suka samu shiga makarantun lauya cikin gaggawa.

Babban sakataren hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Borno, Malam Bala Isa ne ya bayyana haka ranar Talata a Maiduguri yayin da yake zantawa da manema labarai.

Bala ya ce tallafin na shekarar karatu ta 2021/2022 ne.

“Wannan wani ɓangare ne na jajircewar mai Girma Gwamna wajen taimaka wa bangaren ilimi da kuma taimaka wa daliban Borno a kowane mataki na ilimi.

“Muna godiya ga Mai Girma Gwamna da wannan tallafi kuma mun yi imanin da cewa ɗaliban zasuyi iya ƙoƙarinsu don ganin Borno ta yi alfahari dasu,”.

Leave a Reply