Gwamnatin Jihar Bauchi ta tabbatar da bullar cutar ƙyandar biri.

0
172

 

 

Shugaban Hukumar kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Bauchi, Dakta Rilwanu Mohammed, ya ce “Hukumar ta tabbatar da bullar cutar ƙyandar biri a Jihar.

A lokacin da ya ke shaida wa manema labarai a ranar Juma”a a Jihar ta Bauchi Muhammad ya ce “Akwai wasu mutane biyu da ake zargi.

Sa ido tare da bincike
ya taimaka an gano mutum ɗaya yana ɗauke da cutar, yayin da wasu biyu kuma ake duba su.

“Majinyacin ya fito ne daga Adamawa kuma a halin yanzu yana samun kulawa a ɗaya daga cikin cibiyoyin da ke Jihar.

“Ba za mu bar shi ya tafi ba har sai mun gamsu da halin da yake ciki don kada ya cuci wasu.

Ya ƙara da cewa, “Ba kamar kwalara ba inda za a jira kimanin mutane 15 kafin a bayyana bullar cutar, tare da tabbatar da bullar cutar guda ɗaya, za ka iya bayyana bullar cutar ta Monkey Pox,” in ji shi.

Sai dai ya tabbatar wa jama’a cewa Hukumar tare da haɗin guiwar Ƙungiyoyin raya Ƙasa na ƙoƙarin daƙile yaɗuwar cutar.

Mohammed ya kuma bayyana cewa, an ƙara sa ido domin ganin an yi maganin waɗanda ake zargi da laifi nan take.

Haka kuma ya yi kira ga jama’a da su duba alamun cutar domin samun ingantaccen tsarin kula da lafiya.

Mohammed ya lissafa alamomin da suka haɗa da: zazzaɓi, ciwon kai, da ciwon baya, kumburin ƙwayoyin lymph; sanyi da gajiya.

Ya lissafta wasu kamar haka: alamomin numfashi da ƙurji mai iya kama da pimples ko blisters da ke fitowa a fuska, cikin baki da sauran sassan jiki.

Leave a Reply