A yau Laraba ne Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, da jagororin hukumar su ka karbi baƙuncin wasu maziyarta daga ƙungiyar ƙasashen Kwamanwal masu duba shirye-shiryen gudanar da zaɓe.

Tawagar maziyartan sun zo ne a ƙarƙashin jagorancin Mashawarciya kuma Shugabar Sashen Afrika na ƙungiyar, Ms Abiola Summonu,

domin su tattauna kan shirin da hukumar ta yi zuwa yanzu kan Babban Zaɓen shekarar 2023 da za a yi a Nijeriya.
A nan, hotunan da aka yi ne a lokacin ziyarar.