Daga Abu Usaimin
Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa wato (NDLEA) sun kame Alhaji Ademola Afolabi Kazeem mamallakin otel ɗin Adekaz. A kwanaki goma da suka gabata ne, hukumar ta bayyana shi a matsayin babban mai laifi, saboda safarar miyagun ƙwayoyi da yake tare da haramtattun kuɗaɗe.
A jawabin mai magana da yawun ƙungiyar wato Femi Babafemi ya bayyana cewa, sun kai samame ne gidan wanda ake zargin a ranar Alhamis 10 ga wannan watan da muke ciki kuma a yanzu haka yana tsare a ofishinsu.
Wanda ake zargin ya ƙi amsa gayyatar da hukumar ta yi masa, har sai da ta kai kotu ta ba da izinin a kamo shii. Ana zargin shi da taimaka wa wasu da suka yi yunƙurin safarar hodar ibilis haɗe da wasu miyagun ƙwayoyi zuwa Dubai da ke Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) da kuma wasu ƙasashe.
Asirinsa ya tonu ne bayan an kama wani direban mota mai suna Bolujoko Muyiwa Babalola, a ranar 27 ga watan Yuni a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Lagos, ya kuma bayyana cewa giram 900 na hodar ibilis ɗin mallakar mai Adekaz ne.
Biyo bayan rashin amsa gayyatar da hukumar ta yi masa babban kotun tarayya ta ba da damar kame dukkan kadarorinsu da ke Lagos da Ibadan. Ta kuma ba da umarnin rufe asusunsa na banki mai ƙunshe da kimanin kuɗi naira miliyan (217,000,000.00).
Hallau hukumar ta kama wata ‘yarkasuwa mai suna Okefun Darlington Chisom saboda ganowa tana da alaƙa da wasu ‘yanƙasar Pakistan guda biyu. Wato Asif Muhammad mai shekaru 45 sai kuma Hussain Naveed mai shekaru 57 bayan da aka kama su a ranar Asabar 5 ga watan Nuwamba, a yunƙurinsu na zuwa Lahole ta jirgin Qatar Airways. An kama su ne tare kilo 8 na hodar Ibilis.
Omeje Oliver wanda ake yi wa laƙabi (David Mark) yana ɗaya daga cikin waɗanda hukamar ta yi gwanjonsu, bayan da aka gano shi yana yunƙurin safarar hodar ibilis kimanin giram 600. An kama shi ne a ranar 31 ga watan da muka yi bankwana da shi. Yana sanyawa ne a ƙarƙashin takalmin mata, daga nan zuwa ƙasar Liberia.
Hukumar ta kama katan-katan na tiramol da ake safarar su zuwa Karachi, da ke ƙasar Pakistan.
Jumullar katan 6 wato ƙwayoyi 479, 900 mai nauyin giram 304, 90. A jahar Ogun ma an kama buhunhuna masu nauyin 3,533 a kilogiram na mata da miji mai suna Jesutofonmi Solomon.
Harwayau an kama wata da ake kira Sandra David ‘yar jahar Rivers da adadi mai yawa na hodar ibilis da kuma kuɗi kimanin 2, 055, 750,00