Hukumar tattara haraji ta babban birnin tarayya, ta ja hankali a kan yaɗa jita-jita

0
49
  1. Daga Fasihiya

Hukumar tattara haraji (FCT-IRS) ta yi Allah wadai da jita-jitar da ake yaɗawa cewa tana raba takaddun ɗaukar aiki. Labarin da ake yaɗawa da manufar zambatar ‘Yan Najeriya.

A saƙon da ya fitar shugaban mai kula da ɓangaren sadarwa malam Mustapha Sumaila, ya ce hukumar ba ta ɗaukar sabbin ma’aikata a yanzu haka, don haka kowa ya kula kada ya faɗa hannun ‘yan damfara.

Ya ƙara da cewa ko kaɗan hukumar ba ta sayar da aiki. Don haka duk wanda ya nemi da a ba shi wani abu kafin ɗaukar aiki, to mazambaci ne. A kai ƙarar shi ga hukuma.

“Kuma duk wanda ya tallata waɗannan mazambata, to ya yi ne wa kansa ba wani ba. Hukumar ta sanya wasu ƙa’idojin da su ne ma’aunin cancantar mutum ko akasin haka. Kuma tana ƙoƙarin ta ga an samar da adalci a yayin ɗaukar.”

“Ya kamata mutane su riƙa bibiyar labaran da hukumar take sakawa a shafukanta.
http://www.fctirs.gov.ng da kuma [email protected]

Leave a Reply