Hukumar Zaɓe ta ƙaryata zargin ta hana mutum milyan 7 kammala rajistar mallakar katin zaɓe

0
194

Hukumar Zaɓe ta ƙarya mutum milyan 7 kammala rajistar mallakar katin zaɓe Sati ɗaya kafin jam’iyyun da su ka takarar zaɓen shugaban ƙasa su fara yaƙin nan zaɓen 2023, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce ba gaskiya ba ce zargin da ake yi ta tauye wa ‘yan Najeriya milyan 7 damar ƙasara rajistar da su ka fara ta manhajar INEC, domin mallakar katin rajistar zaɓe ba.

Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran INEC Festus Okoye ya fitar, ya bayyana cewa hukumar ta bayar da isasshen lokacin da duk wanda ya fara yin rajistar mallakar katin zaɓe a manhajar INEC, to ya je cibiyar yin rajista ido-da-ido ya kammala rajistar sa.

Okoye ya ce duk waɗanda ba su kammala ba, ko dai sun fara ne su ka watsar, ko kuma sun fara, daga baya kuma ba su kammala ba, sai su ka koma a cibiyoyin rajista ido-da-ido domin su yi a can ɗungurugum.

“An jawo hankalin INEC dangane da wasu rahotannin da ake yaɗawa cewa ana zargin INEC da tauye wa mutum milyan bakwai damar kallama rajistar su ido-da-ido, wadda su ka fara a shafin manhajar INEC ta intanet.

“To ya kamata a sani cewa a gaskiya INEC ba ta tauye wa kowa damar kammala rajistar mallakar katin zaɓe ba. Don haka rahotannin ba gaskiya ba ce, ƙarairayi ne kawai.

“Tun a ranar 24 ga Yuni, 2021 INEC ta ƙirƙiri tsarin fara yin rajistar mallakar katin zaɓe ta manhajar hukumar. Ta yi haka domin rage wa jama’a jeƙala-jeƙala da ɓata lokaci a wurin yin rajista ido-da-ido.

“A bisa wannan tsari, idan mutum ya fara rajista a manhaja, to daga baya zai samu lokaci ya je cibiyar yin rajista ido-da-ido, inda za a ɗauki hoton sa da tambarin yatsun hannun sa, domin kammala rajista, inda daga nan sai ya jira mallakar katin shaidar yin zaɓe (PVC).” Inji Okoye, wanda Kwamishina ne na Ƙasa, kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da kan Jama’a na INEC.

“Mutum 10,487,977 su ka shiga manhajar INEC domin fara yin rajista, amma a cikin su, yayin da 3,444,378 ne kaɗai su kammala yin rajistar a cibiyoyin rajista ido-da-ido.

“Daga cikin 7,043,594 waɗanda ba su kammala yin ta su rajistar a cibiyoyin rajista ido-da-ido ba, mutum 4,161,775 sun yi ƙoƙarin fara yin rajista ta cikin manhaja, amma sai su ka watsar, su ka koma cibiyoyin rajista ido-da-ido su ka yi kai-tsaye.

“Wasu 2,881,819 kuma sun kammala fara rajista a manhaja, amma ba su kai kan su cibiyoyin rajista ido-da-ido sun kammala ba.” Cewar Okoye.

Idan ba a manta ba, kwanan baya ne dai ƙungiyar SERAP ta jagoranci wakilcin mutum 24 waɗanda su ka shigar da INEC ƙara a Babbar Kotun Tarayya, Abuja, su na neman kotu ta tilasta wa INEC cewa ta ba su dama, su da sauran ‘yan Najeriya milyan 7 su kammala yin rajistar su da su ka fara.

A ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1662/2022, sun shaida wa kotu cewa ba su samu damar kammala rajistar su ba har wa’adin da INEC ta gindiya za a rufe yin rajista ya cika.

Leave a Reply