Hukumar ta mai dan mutum 10 bakin aikinsu, ta sauya hukuncin mutum 2 daga kora zuwa ritaya, sannan ta yi watsi da ƙararraki 6.
Hukumar ‘yan sanda ta mayar da mutum 10 kan aiki bayan sauraren ɗaukaka ƙararraki 18. Sannan ta mayar da hukuncin mutum 2 daga ciki zuwa ritaya ba kora ba. A gefe guda kuma mutum 6 ta yi watsi da ƙarar tasu saboda rashin gamsassun hujjoji.
Hukumar ta zartar da hukuncin ne a taronta na ƙasa karo na 17 da ta yi a Abuja, wanda ya ƙare a ranar Juma’a 11 ga watan Nuwamba 2022. Zaman da ya gudana ƙarƙashin jagorancin shugaba ta riƙon ƙwarya Maishari’a Clara Bata Ogunbiyi, JSC(rtd) CFR.
Hukumar ta sake mayar da ƙwararru a sashen ICT 301 zuwa ga sashin aiki na bai-ɗaya. Ta kuma yi ƙarin matsayi na musamman ga sifirtanda (CSP) Daniel Amah zuwa ga matakin gaba wato mataimakin kwamishinan ‘yan sanda (ACP) sakamakon namijin ƙoƙarin da ya yi na ƙin karɓar rashawar dala $200,000.00 a lokacin da yake bakin aiki a matsayinsa na DPO a Bompai da ke Kano. An kuma ba shi lambar girmamawa tare da zunzurutun kuɗi naira miliyan ɗaya.
A dai zaman kuma aka ƙara wa jami’ai kimanin 48 matsayi. Shugabar ta riƙon ƙwarya Maishari’a Ogunbiyi ta bayyana cewa hukumar za ta ci gaba da zaman irin wannan, domin tabbatar da cewa dukkanin ƙorafe-ƙorafen da aka shigar na jami’an da aka dakatar ko aka kora an zartar musu da hukuncin da ya dace don gudun zaluntar su ba bisa haƙƙi ba.
Ta ƙara da cewa za a ci gaba da ƙarin girma akai-akai, amma kuma ta jawo hankalin jami’an da su zage dantse wurin yin aikinsu. Sannan kuma su ƙara himma da kulawa.
Maishari’a Ogunbiyi ta ce akwai ayyuka da yawa da ke gaban hukumar, ya kamata a ce an kammala su. Don haka akwai buƙutar sadaukarwa daga jami’an.