Labarai

Shugaban INEC ya gargaɗi ma’aikata su yi aiki da gaskiya a zaɓen gwamnonin Bayelsa, Imo da Kogi

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya gargaɗi ma’aikatan sa da su tabbatar da cewa sun yi aiki bilhaƙƙi da gaskiya wurin gudanar da zaɓen gwamna da za a yi a jihohin Kogi, Imo da Bayelsa a ranar Asabar mai zuwa.

Yakubu ya yi wannan gargaɗin ne a lokacin da ya kai ziyarar dubagarin tabbatar da irin shirin da aka yi wajen gudanar da zaɓuɓɓukan a jihohin uku.

Shugaban ya tabbatar da cewa za a biya dukkan ma’aikatan dukkan alawus ɗin su kafin a fara zaɓen.

Wannan bayani ya na ƙunshe ne a cikin wata mujallar da ke ɗauke da rahotannin aikace-aikacen INEC na yau da kullum, wadda hukumar ke wallafawa.

Yakubu ya ƙara da cewa INEC ta himmatu sosai wajen wanzar da ingantacce kuma sahihin zaɓe a jihohin uku.

Ya ce: “INEC ba jam’iyyar siyasa ba ce, kuma ba ta da wani ɗan takara daga cikin masu takarar gwamna a jihohin uku.

“Abin da za mu tabbatar shi ne mu himmatu domin tabbatar da gudanar da zaɓen da zai gamsar da jama’a cewa mutane sun zaɓi duk wanda su ke so. Kuma da ma nauyin da ya rataya a wuyan mu shi ne mu kare dukkan abin da jama’a suka zaɓa.”

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button