Daga Abu Usaimin
Ƙasurgumin jagoran ‘yanta’adda wanda aka fi sani da Maikasuwa, ya rasa ransa a hannun jami’an tsaro a wani batakashi da suka yi a ƙaramar hukumar Chikun da ke jahar Kaduna. Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Samuel Aruwan ne ya tabbatar da wannan ƙoƙari a jawabinsa na ranar Juma’a a Kaduna.
“Bayan tsawon lokaci yana gudanar da ayyukan ta’addanci tare da kuɓucewa jami’an tsaro, a yau gwamnati na bugun ƙirgin sanar da al’umma kawo ƙarshen Dogo Maikasuwa da ta yi.”
“Wannan hoɓɓasa ya faru ne bisa wani sumame na hukumomin jami’an tsaro. “Binciken ƙwaƙwaf ya nuna luguden hare-haren da ya kai a wurare masu wahalar ganowa.”
Dogo Maikasuwa wanda kuma ake kira da ‘Dogo Maimillion’ ya jagoranci hare-hare mabambanta da kuma garkuwa da mutane a tsakanin hanyar Kaduna zuwa Kachia, da kuma garuruwa tsakanin ƙananan hukumomin Chikun da Kajuru.
Kwamishinan ya bayyana cewa ɗanta’addar na ɗaya daga cikin ‘yan’amutun a harkar ta’addanci,
waɗanda suke jagorantar harkokin ta da ƙayar baya a ƙasa. Kwamishinan ya ce kusan koyaushe Maikasuwa yana sanye da kayan sojoji ɗauke da bindiga ƙirar AK47.
“Wannan ita ce shigar da jami’an tsaro suke riske shi da ita, a yayin karon battar da suka yi da shi.” A mafi yawan lokaci Maikasuwa yana sanya a kashe wanda aka yi garkuwa da shi idan aka yi jinkiri kawo kuɗin fansa.
A batakashin da suka yi da jami’an na ƙarshe, ƙasurgumin ɗanta’addan shi da magoya bayansa sun yi yunƙurin guduwa dajin Gengere-kaso a tsakanin iyakar Chikun da Kajuru. Aruwa ya ƙara da cewa “Bayan jami’an tsaro sun samu nasarar gamawa da ‘yanta’addar, sun samu bindigar AK47 guda ɗaya, magazine ɗaya, harsashi dunƙulen guda biyar, babura guda biyu, da kuma kakin sojoji. Ragowar yaran nasa sun samu nasarar tserewa da raunuka a jikinsu.
Wani daga cikinsa ma ya rasu sakamakon raunin da ya samu.” Aruwan ya bayyana girmamawar da gwamna malam Nasir Elrufa’i ya yi wa jami’an bisa namijin ƙoƙarin da suka yi.