Juma’ar da za ta yi kyau: Ƙungiyar TIGMEIN da Kyawawan Manufofinta ga mabiya ɗariƙar Tijjaniya

0
200
Shehi Tijjani Sani Auwalu Shugaban kungiyar TIGMEIN na kasa

 

Daga Bilkisu Yusuf Ali

Yayin tattaunawa da shugaban ƙungiyar TIGMEIN Shehu Ahmad Tijjani Sani Auwalu ya bayyana dalilansa na kafa ƙungiyar TIGMEIN , da manufofin da aka dora kungiyar a kai.

Sau tari idan aka kafa qungiya daga manufofin ƙungiyar ake gane shin wannan ƙungiyar kwalliya za ta biya kuɗin sabulu ko a’a. Ƙungiyoyi da suka yi nasara suka sauya rayuwar al’umma suka ka kai su ga fagen cigaba sun sauya su ne da kyawawan manufofinsu. Ire-iren waɗannan ƙungiyoyi suna aiki ne tuquru don tabbatar manufofin qungiyar.

Kamar sauran ƙungiyoyin qungiyar TIGMEIN an kafa ta ne bisa doron gwala-gwalan manufofi da za su kawo cigaba ga mabiya xariqar Tijjaniya. Ƙungiyar TIGMEIN ita ce qungiya ɗaya tilo da take xauke da wannan manufofi ga mabiya ɗariqar don kuwa manufofinta ya saba da sauran manufofin kungiyoyin darikar Tijjaniya .

Da yawa daga cikin kungoyoyin da ake da su a cikin darikar kowacce tana da wani aiki da takr aiwatarwa. Kamar shirya taron zikiri ko shirya mauludi na kasa kokuma tuntubar yan ɗarikar da shawarwari. Amma TIGMEIN an samar da ita ne don tallafi ga ‘yan ɗarikar ta abin dogaro da kai ko bayar da ilimi. ‘Yan xariqar Tijjaniya sun jima suna fatan irin wannan tafiyar ta a gudu tare a tsira tare .

Don haka kungiyar TIGMEIN ta dukkanin xan ɗariqar Tijjaniya ce kuma za ta tafi da duk xan xariqar Tijjaniya babu wani vangaranci ko gidan wane, ko ban da zawiyyar su wane. Kofar qungiyar a buxe take don kowa ya shigo a yi wannan tafiyar da shi.
Kaɗan daga cikin manufofin wannan qungiya sune:
Babban manufar wannan qungiya shi ne haɗan kan dukkan ‘Yan ɗariqar Tijjaniya don yin tafiya da murya xaya. Ta yin haka ne za a fuskanci me Tijjanawa ke buqata, me ne matsalolinsu kuma ina za su dosa don kai ƙorafinsu.

Wannan ƙungiya ta TIGMEIN za ta yi aiki tuquru don tattara bayanai da adadin ‘Yan ɗariqar Tijjaniyya a Niijeriya. Don haka ta samarda website wanda ake fatan tattara dukkan bayanai na dukkan dan darikkar Tijjaniya. A duk inda yake da sunan zawiyyarsa. Su kansu zawiyyoyin an yi musu shiri na musamman inda a duk inda ka ke za ka sami bayanin zawiyar da ka ke nema da dukkan bayananta kai tsaye.

Wanda wannan aiki tuni ya yi nisa. A wannan website din akwai dukkan bayanan da ake nema dangane da Xarikar Tijjaniya.
Yana daga cikin manufar wannan qungiya shi ne wayar da kan ‘yan Tijjaniya sanin mecece haqiqanin xariqar Tijjaniyya da Faira.

Za a yi hakan ne ta hanyar xaukar nauyin darussa a kafofin yaɗa labarai. Sannan wannan hanyar dai ita ce ta janyo hankalin wanda bai ma san me ne Ɗariqar Tijjaniya ba, ya fahimci ɗariqar sannan ya kore masa wasu shakku da qaiqayi da yake ji daga nesa.
Yin wani hovvasa don samar wa da matasa aikin yi da jari don yin sana’a da ma gurabe a matakan gwamnati in dama ta samu.
Ilimi musamman abin da ya shafi dukkan vangarori na shari’a da ibada fage ne da tuntuni ya shahara a vangare na sufanci. To amma duk da haka an ce “in kana da kyau ka qara da wanka” Yana daga cikin aikin wannan qungiya ci gaba da wayar da kan Tijjanawa akan al’amuran zamani da kuma qara xamara kan neman ilimi na addini da na zamani,

Wanda wannan qungiya za ta kakkafa makarantu na din-din-din da ma makarantu na tafi da gidanka, don ci gaba da koyo da koyarwa musamman ga ‘yan’uwa mata da matasa.
Zamani aka ce riga! Siyasa ta zo mana Nijeriya kuma babu ranar bari.

‘Yan Tijjaniya suna da kaso mafi yawa a qasar nan da suke fita su yi zave. ‘Yan Tijjaniya suna zave kuma ana zavarsu. Wanne sakamako suke samu a matsayinsu na masu zaɓe?

Haka yayin da suka fito takara wacce kara ‘yan’uwaTijjanawa za su yi musu? Su kuma wanne alkawari suke ma ‘ya’uwa Tijjanawaa matsayinsu na ‘yan’uwansu in sun samu nasara a zabe? TIGMEIN za ta nazari ta zaɓi mutum na gari sannan a yi wata yarjejeniya ta samar wa ‘yan qungiyar TIGMEIN aikin yi a kowanne vangare na gwamnati a bisa waccar yarjejeniya bayan an kafa mulki. Yin hakan yana cikin manufar TIGMAIN.

Tijjanawa da suke kan manyan madafun iko da dama suna da kishi da son su taimakawa ‘ya’uwansu ta kowanne vangare da suke da dama amma rashin ina za su dosa shi ya zame musu tarnaqi. Sannan kuma a ƙungiyance rashin jagoranci da haɗaɗɗiyar qungiya da za a aminta da ita shi ma duk ya hana a taimaki juna ko taimakon ya kai inda ake fatan ya je.

Amma yana daga aikin TIGMEIN neman inda za a dosa kuma yana daga manufarta sada waxannan mutane da masu buƙatar taimakonsu.

Mata sun kasance masu rauni. Akwai hidindimu da kan taso na aure da sauran hidindimun yau da gobe. Yana daga manufar wannan qungiyar aurar da mata sannan kowacce a kai ta dakinta da sana’a don tallafawa kanta da ma maigidan.

Iyayenmu Shehunnan darikar Tijjaniya yawo suka yi suka yi hidima suka yada addinin Musulunci da darikar Tijjaniya. Ta wannan aka ji amon darikar a dukkanin fadin duniya ba iya Afrika ba. Don haka wannan kungiya daga cikin manufarta har da samar da motoci. Akwai mutane da suke da ilimi wanda ya kamata a ce an karfafe su, su shiga birni da kauye su wayar da kan mutane. Misali yadda ake shiga kauyukan mu da sunan hakika ana bata mana suna. Matasa suna aikata abin da suka so da sunan hakika. Muna da masu ilimi arifai mun tsara mu ba su mota da ‘yan kuxaxe suke shiga saqo da lungu, jiha-jiha don aiki tukuru don kamanta yadda magabatanmu suka yi sannan an samar da aikin yi an yaxa ilimi an yaxa alheri an kawar da jahilci da bata- gari.

Muna son mu kawo cigaba da tsari mu kafa wani abu da yaranmu da jikokinmu za su amfana a zuwa gaba saboda mu muna son mu reni kungiya ne don bayanmu ta amfana wanda haka ya kamata al’umma ta kasance.Muna son yau idan yaranmu sun haddace Al’kur’ani to me ya kamata su yi a gaba.cigaban al’ummarmu yana gaban kowa. Don haka wannan kungiya za mu raineta ne don goben yaranmu ta yi kyau. Mun sauke nauyi da amana da Allah ya dora mana da damar da muke da ita a yanzu.
TIGMEIN ba jam’iyyar siyasa ce ba, kuma mu ba za mu yi siyasar jam’iyya ba amma dai in mun ga namu wanda yake da buri da karfi a cikin darikarmu, kuma mun san namu ne dari bisa dari kuma yana da kishinmu, to za mu qarfafe shi kuma mu yi aiki tukuru wanda wannan aikin da muka yi da kudinmu da jikinmu da kwakwalwarmu in mun ga wanda zai adalci za mu ce ga namu kuri’un wanda in aka ci mu ma akwai namu bukatun.

Bayan aikin kasa, kamar muna son jami’a a yi mana lasin ga wani namu a yi masa minister ko kwamishina ko a gina mana makaranta ko masallaci ko a dauki yaranmu da suka yi karatu aiki ko a samar musu gurbin karatu da dai sauran bukatu na yau da kullum karkashin wannan kungiya ta TIGMEIN.

Don haka kungiyar TIGMEI

kungiya ce da ta zo da kyawawan
manufofikuma kofarta a bude take ga dukkan wanda yake da tambaya ko nemna Karin haske kokuma yake son ya shigo a yi tafiyar da shi.

Leave a Reply