____________________________
*👩🦱 KALLON KITSE book 1👩🦱*
*NA HALIMA ABDALLAHI K/MASHI*
*Page 2*
*Wannan littafin na kudi ne masu son document Complete 1&2 500 masu son pages 300 zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻
“`ACT<<0700549935
Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925“`
*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*
*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427_*
Washe gari saida inna taje kasuwa tasaiwa uwani sabbin kaya na kanti, kala bakwai, sai silippers. Tasa indo ta tsefe mata kanta. Indo tsab ta kwance kan, ta wanke shi tas, nan danan ta canza, tayi kyau, inna tace toh ko kefa, duba kiga yarinya da sha’awarta, amma sam bata samu kula ba, zo uwani inji inna, ta kalli inna ta tako inda take, ta rike hannunta tace kina zuwa makaranta kuwa? Uwani tace a’a.
Toh islamiya fa? Ta karace a’a muna zuwa na allo.
Ok wace sura kike a makarantar allon?
Kulhuwallahu. Tace toh yayi kyau.
A lokacin jafar ya shigo ya zauna ya dubi inna ya gaidata da kwana, wai yaushe zaka koma makarantar ne? Yace ai sai next weeak.
Ok zamu shiga insha Allahu, toh dama so nake anema wa uwani makaranta nan kusa damu, ya dubi Aisha wanda tun shigowarsa ta nutsu, tun jiya ta gane shiba na wasa bane.
Toh basai asata makarantar nan ta high standard ba, kin san inna tanada kyau.
Eh gaskiya ne, sai kaje ka bincika, dama a yanzu first term ake dauka kafin ayi nisa.
Da yamma likis ya dawo ya shigo, ya iske uwani batada riga, daga iita sai dan wando, yayi mata tsawa ke ina rigar ki? Jikinta na rawa ta shige daki da gudun ta, sai bayan dake kwance, ta mike zaune kedawa uwani? Ta nuna bakin kofa. Inna itama kofar take kallo. Jafar ya shigo ciki yana magana, in nasake ganinki baki da riga saina dokeki, yarinya sai kazanta, saikace wata….., inna ta kaste shi “wai kai dan Allah meya dameka da ita? Sam ka hana yarinya sakat, saboda me? To bara kaji gaskiya kada ka takura mata. Yana zaune yana aikin hararar uwani, ita kuma tayi kamar bata wurin dan inna rungumeta tayi akafarta. Ya batun makarantar ka nemo?
Eh na nema, har na na biya kudin makarantar, gobe zan kaita insha Allahu.
Toh an gode Allah shiyi albarka, uwani maza kira min indo ta kawo masa abinci, ta kama hanya da gudunta, ta fice daga falon.
Tun daga ranar ta fara zuwa makaranta, ansata nusery one, cikin satin da kyar take barin inna saboda kukan, ta ba zataba, saida jafar yayi da gaske, dan ranar saida ya doketa, inna kuma in banda fada ba abunda takeyi, tace ma bazata ba, saida indo tasa baki. Inna ta maida indo abokiyar shawaranta, saboda ta fahimci indo mutum ce mai rike alkawari, kuma ba munafuka bace, sun sami kusan shekaru shidda tare, amma sam basu taba samun sabani ba a tsakanin su, a ko da yaushe indo tana gudun zuciyar inna, shiyasa suke zaman lafiya.
Jafar ya koma makaranta don haka yasa uwani keyin abunda taga dama, musamman inna ta dauki direba yana kai uwani makarantar boko da islamiya. Yadda uwani ta zmz yar gata gun inna yasa yarinyar har shagwaba ba wanda batayi, bazaka taba cewa bata da jini da inna ba, da yake inna ta dauketa tamkar yadda ta dauki jikokinta, harma ta hadasu da sauran ‘ya’yanta, dan in sunyi waya idan tana kusa saita bata su gaisa. Har suma suna tambayarta in suna magana.
Abunka da mai jiki mai saurin girma, nan da nan cikin ‘yan kwanaki uwani ta warware, tayi kibanta gata bul-bul gwanin sha’awa, gata da saurin shiga rai, saboda suffanta irin ta larabawa ce, duk da ita ba fara bace, wakan tarwada ce, amma msi haske, ga gashi irin mai murdewan ga cika, saidai uwani bata son abinda ya taba mata kai, kullum sai sunyi da gaske, za’ayi mata kitso. Inna dole ta rinka sa indo tana lallaba mata kan, shima sama-sama, dan haka ne kullum zaka ga kan a yakuce, sam inna bataso taji kukan uwani ko akan menene, uwani gata da surutu kamar me, inna kam har ta saba dan kullum suna tare bata zuwa ko ina, indai ta dawo gida toh tana manne da inna.
Mal. Mamman sunan direban inna, zai iya kai shekaru hamsin da wani abu, yanada iyali anan cikin garin, saidai matarsa ta dade da rasuwa, tanada ‘ya’ya bakwai, tare dashi. Dukkansu matan sunyi aure, da yake ‘ya’yan sa maza biyu ne, kai su suka rage, shi yana son auren indo, ita kuwa indo sam taki ta amince kuma taki ta fada dalili.
Inna na zaune a daki taji ana sallama daga can falonta, tace uwani, maza jeki fadi waye? Ta fita a guje, kamar ma zata fadi, inna tace, wai uwani bana hanaki guje-gujen nanba, salon kije ki fadi ko? Ina? Uwani kam bata saurara ba, tanufi falon ta iske mal. Mamman, ta fada jikinsa tana fadin baba dama kaine, inna tace in duba wanda ke sallamar?
Eh nine jeki fada mata. A guje dai ta koma sukai karo da inna, toh ‘yar fama nidai kar kije kiji ciwo. Ta karasa falon, ta zauna, uwani ta dare kan cinyarta, tace a’a mal. Mamman kaine ashe, ka wuni lafiya?
Lafiya lau inna”
ina fata ba uwani ta kara yin wani abun a makarantar bako? A’a inna aita daina.
Kasan Allah bata daina ba, don da naje opening day dinsu, saida malamar takara min magana akan uwani bata daina dukan yaran mutane ba, harda cizo takeyi. Mal. Mamman yayi dariya, inna zata daina, yarinta ke damunta, amma kam Aisha akwai ta da fada, shiyasa nake sonta, saboda tsiwanta, ga iya lafazi kamar wata babba, koda yake tana tare da manya dole ta iya, yaci gaba, dama inna wata magana ce ta kawoni, mai muhimmanci, don Allah inna dama…..dama indo ce nake so, amma sam taki amince min, yanzu haka satina uku kenan ban sata a ido ba, nayi da ita ta fadamin dalilinta, amma taki shine nace bara na biyo ta wurinki, kila ta amince. Inna ta gyara zama sosai, ta kara gyarawa uwani kwanciya, dan tuni tayi barci, akafan innar, toh mal. Mamman gaskiya ne, kuma haka yayi kyau, in Allah ya yarda zanyi mata magana, kuma zan nemeka. Allah yasa Alheri a wannan batu, Allah kuma yasa damu za’ayi ameen.
Bayan tafiyarsa inna har daki tabi indo, indo tace ita bawai auren ne bata soba, ita bata so ta bar gidan, inna tace, wannan mai sauki ne, saiku zauna a boys quater, tunda ba kowa anan. Ahaka inna ta kwantar wa da indo hankali, har ta amince da maganan auren mal. Mamman.
Washe gari ta nemi mal. Mamman ta fada masa yadda sukayi, yaji dadi sosai dan dama gida haya yake zama, yanzu ya huta da biya, yayi godiya yace, saita taimaka ta tambayeta yadda takeso ayi, dan gaskiya inaso a daura kafin azumi. Inna tace hakane, yau fa saura kwana goma sha bakwai a fara, dan hka ninasa ranar nanda sati biyu, mal. Mamman ya washe baki yana godiya, inna ta kara da cewa kaje ka duba dakunan, ga makulli, Allah yasa an dace. Ya amsa yana godiya.
Abu anyi shi a saukake, dan haka komai yayi sha’awa, indo ta tare a dakinta, harma inna ta bata kyautan set din kujeru da gado, komai yayi acan-acan.
Jafar ana saura kwana biyu a zumi ya dawo gida, ba wacce ya sawa ido irin uwani, saboda acewarsa ta cika shagwaba, komai tayi, sai ya kusheta, tun da tazo gidan yau watanta kusan bakwai, amma bata daina kazanta ba, makaranta kuwa tana dai nata kokarin amma ba sosai ba, shiyasa yake yawan tsawata mata.
Ita kuwa data lura da hakan, indai tasan yana gida saita gudu can sashen indo, tayi zamanta.
Azumi na saura kwana daya ya kare jibi sallah, salaha da ‘ya’yanta suka dira sokoto, dama tuni mal. Mamman yaje ya tarbesu, ana sallar azahar suna shigowa, inna tasa indo ta shirya abinci kala biyu, ga fura kuma da sinasir, don haka yaran sunji dadi kwarai don suna son irin hurar inna. Salaha tace gaskiya inna kinyi dacen yarinya, ta maidake uwa.
Inna tace kinsan dama tun can ‘yar shagwaba ce shiyasa, hafsat da uwani da yake suna sa’annan juna, nan da nan suka shaku da junan su, suna wasa.
Washe gari zainab ma ta ison gidan tare da ‘ya’yanta baki dayan su, da yake shima mijn ya gina gida musamman saboda insun zo su zauna, shiyasa basu barin kowa. Alokancin ne suka hadu su uku ina nfin uwani, hafsat, da kuma fa’iza, duk da duk sun girmeta amma tafisu baki, ga tsiwa, amma ba karfi. Inda uwani ke sa’an cinzali shine, saboda tsiwarta, dolene ako da yaushe sai su rinka fada da hafsat dan itama ba kyalle bace, har gwara fa’iza dako tsokananta kayi ba ruwanta.
Ranar sallah bayan andawo idi, jafar ya shigo gidan, nan da nan yara sukaje gunsa suna fadin uncle barka da sallah. Saida ya bawa kowa, amma banda uwani, idonta yayi rau-rau zatayi kuka, ya daka mata tsawa, in kikayi min kuka saina gurje bakin nan naki. Salaha tace “haba jafaru ya zaka bawa kowa nasa banda ita, kuma kace kar tayi kuka? Inna tace ‘eh ai gara kitayani fadi, in gaya miki auta sam baison diyar nan tawa, zo uwani ki karba, ya shiga ya zauna tare, da fadin salaha don Allah dubi yarinyar nan kazamiyace wallahi, ki duba kiga hafsat da fa’iza anyi musu kitso, sannan kayan jikinsu komai tsab, ita fa? Dubeta kanta babu kitson kwarai sannan ta cire zaninta ta yar, dubi fuskarta ki gani, duk majina ina zan bata barka da sallah?
Inna tace babu ruwanka da ita, haka kawai yarinya karama batada ikon sakewa itada gidansu, kaidai sonkai kake nunawa, toh ta Allah ba takaba, ni wallahi na matsu ka koma makaranta mu huta, tunda kadawo ka ishemu da masifa, ko an gayama bana lura da yadda duk ka takura mata?
Salaha tace. Kaiko jafar ka bawa kanka lafiya, kaima kasan sai a hankali uwani zata daina behaving haka.
“kinsan Allah salaha, wannan yarinyar bazata dainaba, ai kazanta halittace…”
“bari kaga irin yaran nan sunfi kowa kwalliya insuka girma, yarinta ne ke damunta.
Ya mike tsaye yana fadin toh haka dai kukace , ai muna nan zamu gani.
Lokacin zainab ta shigo, uwani ta ruga aguje tanayi mata oyoyo aunty. Aiko saita fadi kasa, jafar da karfi yace Allah ya kara. Inna da sauri ta mike tunkan salaha takai harta dauko ta, da yake inna jikinta mai iri kyan nan ne, bazaka taba yarda takai hamsin da biyar ba, don kyan jikinta, batada kiba dai-dai take. Wurga wa jafar harara, batace komaiba, amma ta rungume uwani ta lallashi, shikuwa jafar mikewa yayi dan yasan ya batawa inna rai, ya fito waje yaci karo dasu bashir………..
#######