Na ja tsaki bayan na ƙwanƙwasa ƙofar gidan kusan sau biyar, bisa ga dukkan alamu bata nan. A fili na ce rainin hankali matar nan dan iskanci bata nan amma ta ce min inzo ta na gidan!
A fusace na ciro wayata da zumar in kira in fece ta, amma sai ga kiran ta ya riga shigowa, ina ɗagawa ta rigani da faɗin. “Yi haƙuri Aminiyas na je nan titi ne in karɓo kayan miya ke zan yi wa awara yi haƙuri.
Zanyi magana ta sake tare numfashi na da cewa “Har da ƙwai zan miki gani nan. Ta kashe wayar. Na yi guntun murmushi sannan na zauna a dakalin ƙofar gidan ina faɗin Aminiya uwar wayon tsiya, tasan tun da ta ambaci awara dole in tsaya.
Da gudu yara biyu suka fito daga gidan da ke kallon na ta, su ka kaure da faɗa. Daga inda na ke na daka musu tsawa, amma basu san ina yi ba, ganin an buga ɗayan da ƙasa ya saki ihu sai na tashi naje zan raba su. Sai ga wata mace da gudu ta fito daga gidan tana faɗin “Wallahi ka rama shima sai ya yi kuka.” Ga mamaki na ta riƙe yaron wai ɗanta ya rama. Yaron ya kafa masa cizo a damtse, ta ke ya saki ihu, sai ga wata matar da gudu da alamu uwar wanda aka ciza ce. Ta ce aiko bazan yarda ba ta kai hannu zata kamo wancan yaron Tana faɗin Nasiru kai ma sai ka ciki Ali, sai kuwa uwarshi ta kai wa rigar ta damƙa.
Nan na ta ke suka shiga dambe. Mutane suka taru, kafin a raba su an yi wa uwar Nasiru dukan tsiya har jini na tsayuwar ta bayan kunne. Ƙawata ta iso ina faɗa mata,ta ce kullum sai sunyi dambe akan yara in dai waɗannan ne.
Ta kama hannu na wai mu shiga gida, sai kuma ga mai laifin da Ɗan sanda. Na ce dubi kuma ita ce da kiran Ɗan sanda. Ƙawata ta ce Maman Ali ai akan Ali babu abinda bazatayi ba.
Ita kuma Uwar Nasiru tace baza ta bi Ɗan sanda ba. Sai kuma sabon faɗa ya tashi, in taƙaita muku dai sai ga Ɗan sanda suna shan dambe da mata wai sai ya jata. Allah ya bata sa’a ta yayyaga masa koɗaɗɗun yinifom ɗin ta huce haushin dukan da Maman Ali ta yi mata.
Na Kalli ƙawata Lami bayan mun shiga gidanta, na ce yanzun yaya matar nan zata ƙare da ta duki Ɗan sanda? Lami ta ce oho Nima dai abin ya dame ni.
Kamar kimanin awa ɗaya da shigowar mu, muna cin awara muna labarin kasuwancin mu, sai muka jiyo kukan motar ‘Yan sanda da gudu muka ja mayafai muka leƙa. ‘Yan sanda sun kai shida suka ɗuru cikin gidan. Muma muka shiga domin kar a bamu labari.
Muna shiga na ga matar da ta doki Ɗan sanda kwance cikin jini tana ta nishi, suma ‘Yan sanda suna tsaye suna kallon ta tare da tambayar abinda yafaru.
Wata mata wadda bangan ta ba lokacin da ake kwasar faɗan ƙatuwa mai suffar mafaɗata ta fito ta shiga ba ‘Yan sanda amsa kamar haka.
“Ranka ya daɗe ɗan uwan ku ya zage damtse ya yi ta kirɓar ta kawai saboda shi ɗan uwan abokiyar faɗan ta ne, ta kira shi ya hauta da duka ba jin ba’asi,ga shi yanzu ta yi ɓari anje kiran mota ne yanzu a kai ta asibiti. Wannan ma sai dai babban Asibiti. Ta kai ƙarshen maganar tana kallon Maman Nasiru cikin sigar karaya. “Yan sanda suka koma gefe suna tattaunawa.
Na dubi Lami na ce wai to muna ina lamarin ya zama haka? Ta ce oho. Aka kwashi mata tana numfarfashi aka sa a mota.
Lami ta nufi gurin matar da ke rattafa bayani ta ce Karima uwar dashi wai wa ya daki Maman Nasiru? Mu ai mun shiga gida lokacin da ta duki ɗan san…. Da sauri Karima ta sa hannu ta rufe wa Lami baki sannan ta jata gefe, “Karki furta wannan zancan. Na zo na sami Maman Nasiru ido ya raina fata, wai ta doki ɗan sanda Maman Ali sun tafi su zo da wasu’Yan sandan sai na ce to ita yanzu jira ta ke a zo a tafi da ita. Ta ce wai yaya zata yi, shine na ce bata da hankali nan na kama tattabarun ɗanta na yanka, har guda biyu na ce ta kwanta ta yi ta nishi. Kin san ta na da ƙaramin ciki na kira mijin ta na faɗa masa an dake ta tayi ɓari, iya ka in anje asibiti likita ya ce cikin bai faɗi ba, ko banza dai za a ƙara mata ruwa ta ƙara lafiya, sauran bayani ya rage na mijinta ko dai ya yafe wa ɗan sanda kokuma ya kai kotu.
Na kasa magana dan tsabar mamaki.
Bayan kwana biyu na binciki Lami ko wannaw wutar ta mutu. Sai take bani labarin cewa kwana Maman Nasiru huɗu a asibiti sannan da kyar mijinta ya haƙura tunda ciki yana nan, amma dai ita mara lafiya an kai mata kayan dubiya da wasu ‘yan kudi da aka karɓa daga hannun Ɗan sanda da kuma Maman Ali.