Littafin Rana ɗaya: Feji na 8 Halima Abdullahi k mashi

0
280

📚4️⃣
Page 8

Yana shiga ya samu ta gama shirya kaya a cikin akwatuna, ya zauna a kan kujera daidai lokacin da sako ya shigo cikin wayar da ya saka a cikin aljihunsa. Ya ciro wayar tare da fadin,Nafisa ina son ki sanar da ni ainihin abin da ke faruwa” Idanunshi suna kan fuskar wayarshi don duba kowane sako ne ya shigo cikin wayarsa. Amna ce cikin sauri ya bude yana karantawa.Baban Jafar ina son mu yi magana da kai, amma ba ta waya ba. In abin da na ji da kuma hujjar da aka kafa min da Salma haka ne, to gaskiya ka ba ni mamaki sosai. Kafin in tafi gida ina son sai mun zauna na ji wasu abubuwa daga bakinka. Har yanzun ni na yarda da kai, kuma na sani gaskiya ka ke fada min a kowane lokaci.

Abu daya nike son ka tuna, iyayena mutane ne da ba su son in takura ko in shiga wani hali. Ko babu komai na je na ce musu na gaji da aurenka ka san za su tsaya min a haka. Na tuna maka ne don kasan cewa, in na saka kafa na bar gidanka da sunan na tafi, to ka sani fa na tafin kenan Shatima ya runtse ido yana fadin,” Allahumma ajirni fi musibati’. Ya fita waje ya nufi harabar gidan. Nafisa ta bi shi da kallo, tare da son sanin sakon da ya samu a cikin wayarsa.Munnir ya kira, ko gaisawa bai bari sun yi ba ya shiga fadin,Ina cikin musiba Munnir. Wacce qaddara ce take bina?”

Munnir yace,Me kuma ya sake faruwa?” Shatima ya ce,Ban san komai ba, bansan abin da ke faruwa ba, gabadaya matana sunA min bore, kuma ban san komai game da tuhumar da suke min ba” Munnir ya ce,To ka zauna da su ka ji kan zancen mana Shatima ya ce,Ina Abuja yanzun haka”. Ya ba shi labarin komai a takaice, ya ce,

“Ka taimaka min dan basiran tawa ta toshe ban san me zan yi ba. Ban fahici me kowaccensu take nufi ba Munnir ya ce,

‘”Kira Aliya ka ji, na san ita za ta fada maka komai” Ya ce,Kuma haka ne, don ita ba ta ce wani abu ba Yana kiran Aliya ta daga kamar dama jiransa take yi, ya ce,Aliya me ki ka sani game da abin da ake yadawa a tsakaninku?”

Ta ce, Me ake yadawa?” Ya ce,Nafisa da Amna suna tuhuma ta da wani laifi ko iri daya, ko kuma kowa da nata. Haka kuma Salma ma tana tuhumata kina nufin ke ma ba ki san komai ba?” Aliya ta ce,Ni dai ban ji komai ba gaskiya”Ya ce,To ki tayani da addu’a” Tace,

“Insha Allahu Suna gamawa Aliya ta sa dariya,

“Ai nunawa zan yi ban san komai ba, kuma ba zan canza masa ba ko da kallon banza

Shatima ya nufi ciki gurin Nafisa, da ya shiga dakin nata sai ya kulle da makulli saboda kada yaransu su fito su shigo su same su a dakin. Tana shirya wandunan yaran da singiletinsu a Karamar akwatinsu, ya je har inda take ya ce,Ke madam, bar wannan aikin ki zauna ki ba ni aron hankalinki a nan”

Kamar ta share, amma sai ta cije ta ce,

“Ina jinka” Ya ce,Ina son ki nutsu ki fada min duk abin da ke faruwa, don ban san komai a kai ba” Ta ce,Tunda ba ka sani ba a bar maganar Ya ce, “Haba Nafisa?”

Ya sake tausasa harshensa, “Kin san dai ta hanyar tattaunawa ake warware matsala ko?”

Kallonshi kawai take yi tana takaicin raina mata hankalin da yake yi. Tsaki ta ja sannan ta ce,In har kana nuna ba ka san komai ba, wannan yana nufin ba za ka amsa laifinka ba, wanda kuma amsa laifi malamai sun amince alamu ne na rabin tuba

Shatima ya tsura ma Nafisa ido cikin bacin rai, ya ce,Amma sai a fada min laifin nawa in sanshi ko?”Ita ma ta dube shi a hasale,To tunda so ka ke ka maida ni jahila da ana magana ne a kan Zinatu karuwarka,wadda ku ke watsewarku da ita har ma ka yi mata alkawarin sakin dayarmu ka aure ta.

Marin da ya sakar mata ne ya tilasta mata sakin wancan zancen tare da fadin,Wayyo Allah”Jikinshi har tsuma yake yi, ya ce, “Sharrin da za ki min kenan? To in don wannan zantukan da ki ka kaga min ne zaisa ki tafi ki je. Amma in kin tafi kin tafi kenan, kuma ki bar min yarana a nan babu inda za ki da su” Ya bude kofar ya fita, kaya ya canza sannan ya kwashi yaransa ya zuba a mota suka fice.Sai da Nafisa ta ci kukanta ya ishe ta,sannan ta kira Anty Maimuna tana fada mata.

Anty Maimna ta ce,To yanzun ke tahowar za kiyi?”Nafisa ta ce, “Gobe zan taho gaskiya”

Anty Maimuna ta ce, “*Ba ki da hankali, inkin tafi ai kin ba karuwar dama ta zo gidan ta baje kolinta, kuma ita za ta rike “ya°yanki ko da aure ko babu. Abin da nike so da ke shine, ko yaranki kada ki bari su san kuna da matsala.Haka nan fushinki ba zai kawo maslaha ba. Da ya ce ma ku zauna ku tattauna ban da yarinta da wauta irin taki ai ba za ki kwashi hayagaga ba sai ki yi masa zance cikin hikima da nuna masa illar abin da zai saka kansa kuma ya jefa ku. Ban dake ai wannan kin da ya yi ma alama ce ta ba ya son bacin ranki, mazan yanzun da suke neman mata ina ruwansu da wani boye ma iyalinsu? Kizo barikinmu ki yi kallo, wani sai ya zo da mace ya koro- matarsa waje,

shi ya shiga ciki da karuwa

Leave a Reply