MALAM IBRAHIM SHEKARAU SHUGABA ABIN KOYI

0
56
Malam Ibrahim Shekarau

Daga Bilkisu Yusuf Ali
Chairperson National Women Allience For PDP 2023

A ranar 5 ga watan Nuwannba 2022 Malam Ibrahim Shekarau ya cika shekaru 67 cif da haihuwa. Zagayowar ranar haihuwar ta dace da lokacin da Malam Shekarau yake qamshin turare xan goma a jam’iyyar PDP. Wa ye malam Ibrahim Shekarau , me ne silar farin jininsa da xaukakarsa a fagen siyasa?

An haifi malam Ibrahim Shekarau a Unguwar Kurmawa a cikin birnin Kano, An haife shi ranar 5 ga watan Nuwamba na shekarar 1955. Sunan mahaifinsa Malam Sulaiman Usman , mahaifiyarsa Hajiya Maryamu. Mahaifinsa jami’in tsaro ne, ya yi aikin xan sanda na tsawon shekara 35 a tsarin ‘yan Doka da aka fara yi tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka. Quruciyar Malam Ibrahim Shekarau ya yi ta ne a hannun iyayensa, Malam Ibrahim Shekarau ya fara da karatin allo kamar yadda aka sana a qasar Hausa daga nan ya shiga makarantar firamare ta gidan Makama, Ya yi sakandire da Aminu Kano Commercial College. Da jam’iyyar Ahmadu Bello da ke Zaria daga shekarar (1973-1977) Ya samu takardar shaidar digiri ta farko. Bayan kammala digiri sai ya fara aikin gwamnati. Ya fara da Government Technical College da ke Wudil a shekarar 1978, bayan shekaru biyu ya zama shugaban makarantar Government Day Junior Secondary School a Wudil A shekarar 1980. Ya koma makarantar Government Secondary School, Hadejia. da Government College Birnin Kudu a 1986 da Government Secondary School a Gwammaja da Rumfa College a 1988, duk a matsayin shugaban makaranta.A shekarar 1992 mallam Shekarau ya zama mataimakin darakta a harkar illimi. Bayan shekara guda aka mayar da shi darekta.Ya zama babban sakatare a ma’ikatar harkar illimi.
A watan Fabrerun shekarar 2000, malam Shekarau ya koma aikin gwamnati, kafin a komar da shi kwalejin share fagen shiga jam’ia a matsayin babban malamin lissafi. A nan dai Malam Shekarau ya ajiye aiki da gwamnati bayan ya yi aikin na tsawon watanni 17 a kwalejin.
MALAM IBRAHIM SHEKARAU DA SIYASA
Akwai mutane da ake kira ‘yan baiwa haqiqa malam Ibrahim Shekarau yana cikinsu musamman idan aka kalli irin tasirinsa a siyasa lokaci guda. Da farko ba a xauki Malam Ibrahim Shekarau a matsayin wani xan takara da zai yi tasiri ba a zaben gwamnan da aka yi a shekarar 2003 a jihar, amma daga baya kuma sai ya yi tasiri inda ya lashe zaven. Malam shekarau ya kafa tarihi inda ya zama gwamna na farko da aka zabe shi a karo na biyu a matsayin gwamna a jihar Kano. Malam Ibrahim Shekaru ya zama xan takarar shugaban qasa a jam’iyar ANPP a Zaben watan Afrilu na shekarar 2011. Malam Ibrahim Shekarau ya riqe muqamin ministan Ilimi a zamanin shugabancin Goodluck a qarqashin jam’iyyar PDP. Malam Ibrahim Shekarau ya zama Sanatan Kano ta tsakiya a shekarar 2019 a qarqashin jam’iyyar APC zuwa lokacin da ya bar jam’iyyar zuwa jam’iyyar NNPP bisa wasu dalilai waxanda suka shafi rashin cika alqawari da mutumta zamantakewa ta siyasa daga jam’iyyar APC. Ko a NNPP xin ma hakan ta kuma faruwa, bayan zama da tuntuvar magoya baya , magoya bayan malam Ibrahim Shekarau suka yanke shawarar komawa gidansa na baya wato jam’iyyar PDP. Inda aka san darajar goro nan ake yyayafa masa ruwa. Xan takarar Shugaban qasa a jam’iyyar PDP Alh Atiku Abubakar ya isa Jihar Kano tare da abokin takararsa, Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta da Shugaban PDP na Kasa, Iyorchia Ayu, da sauran shugannnin jam’iyyar na qasa da duk masu faxa a ji a jam’iyyar ta PDP suka shigo takanas don karvarsa a jam’iyyar ta PDP. A bikin , tsohon gwamnan jihar Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana matakin da ya xauka na barin jam’iyyar NNPP da komawa jam’iyyar PDP ya yi shi ne a dalilin yaudararsu da xan takarar Shugaban Qasa na jam’iyyar NNPP, Shekarau ya yi ikirarin cewa jagoran jam’iyyar NNPP bai yi musu adalci ba. dangane da yarjejeniyar da suka qulla kafin komawarsa jam’iyyar.
SARAUTA
Mai martaba sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, ya naxa shi a matsayin Sardaunan Kano a karon farko a tarihin masauratar Kano.

HALAYYAR MALAM SHEKARAU DA TA BAMBANTA SHI DA SAURA
Yana da haquri da kowa ba za ka tava jin malam Shekarau na faxa da kowa ba , ko da kuwa an tsokane shi ko an ci fuskarsa yana kau da kai. Don haka kullum akan ji harshen masu adawa da shi ne amma shi ba a jin martaninsa
Kawaici da ko da abu zai cuce shi zai yi karar.
Shugaba ne da ya yarda da cewa shugabanci sai da jin korafin magoya baya sannan ba ya yanke kowanne hukunci sai ya ji shawararsu, domin ya ba su damarsu. Bai yarda da shugabanci na kama –karya ba. Tun yana gwamna har zuwa yau.
Malam Ibrahim Shekarau bai yarda da cewa siyasa ta marassa kunya ce da surutai barkatai kamar a tasha ba. Don haka ya sa dokar tsarkake harshe da duk abin da za a faxa sai an sa ladabi a ciki an kyautata magana tamkar a masallaci mutum yake, ko da kuwa yana kan diro xin kamfem.
Malam Ibrahim Shekarau ya fara janyo malam addinin Musulunci da xaliban ilimi cikin harkar siyasa don maye gurbinsu da marassa tarbiyyar da suke xaukar siyasa ta marassa kunya ce, da ‘yan boko aqida da marassa ilimi. Kuma hakan ya qara tsaftace siyasa har ya ja hankalin mutane masu daraja ga siyasa ganin irin su malam da muqarraban gwamnatinsa a siyasa.
Kowa ya shaidi malam Ibrahim Shekarau akan kansa ba varawo ba ne. Saboda kuwa irin tsangwama da yarfe da yadda ya zame wa wasu tarnaqi da yana da laifi komai qanqantarsa da sun bi duk inda za su bi su kama shi ko su wulaqanta shi.
Malam Ibrahim Shekarau shi ne mutum xaya da magoya bayansa ke girmama shi don nutsuwarsa da kamalarsa da kyakkyawan lafazinsa ba wai don ruxu ko don farfaganda ba. Masoyan malam duk inda suke za ka iske su nutsattsu da soyayya don Allah ba don kuxi ba ko muqami. Wanna ya sa magoya bayansa ko da sun sami savani na siyasa ba za ka tava jin sun aibata shi ba a fili ko a voye. Shi yana riqe su a matsayin amana kuma uba haka suma sun yarda shi xin jagoransu ne suna jam’iyya guda ko a’a.
Shugaba ne, na mutane don haka gidansa yake a buxe ba a rufe gdansa , yana gari ko ba ya gari. Gidan hedikwata ce kuma fada ce sannan munbari ne na wa’azi da siyasar zamani.
Mai gaskiya ne da saurin sallamawa da yarda da mutane da zama da su zuciya xaya, wannan yana cikin dalilan da ya sa ‘yan siyasar zamani ke sauran yaudararsa.
Bangon sikari kirarinsa kenan. Don kuwa ba wanda zai ravi malam Shekarau bai amfana ba. Babban abin farin cikin da irin kyautar nan da addini ya yi umarni wato ka bayar da kyauta da hannun dama , hagun bai sani ba.

Muna fatan Allah ya ja kwana, ya qara lafiya da xaukaka al’ummar Kano , Al’ummar Arewa da ma al’ummar Nijeriya su ci gaba da amfanar wannan tsiro na albarka amin. Maigirma Sanata Allah ya kai fata mizani.

Leave a Reply