Minista Sadiya ta ƙaddamar da shirin ba manoma da mata ‘yan kasuwa 4,000 rancen shirin GEEP 2.0 a Bauchi

0
188
Hajiya Sadiya Umar Farouq ta na ba da cakin kudi na agaji a shirin Tradermoni a Bauchi

 

Sama da manoma da mata ‘yan kasuwa 4,000 ne su ka fara karɓar bashi maras ruwa a ƙarƙashin kashi na biyu na Shirin Haɓaka Kasuwanci, wato ‘Enterprise Empowerment Programme’ ko ‘GEEP 2.0’ na Gwamnatin Tarayya a Jihar Bauchi.

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta ƙaddamar da ba da rancen kwanan nan a garin Bauchi.

Masu cin moriyar shirin sun karɓi kuɗaɗe da su ka kama daga naira dubu hamsin (N50,000) har zuwa naira dubu ɗari uku (N300,000), kuma ana sa ran su biya rancen ba tare da wani ruwa da aka ɗora ba a cikin wa’adin shekara ɗaya.

A jawabin ta a taron, ministar, wadda kuma ta rarraba agajin tsabar kuɗi ga mutum 5,679, ta yi kira a gare su da su yi amfani da kuɗaɗen wajen yin ƙananan sana’o’i masu riba don inganta rayuwar su.

Ta ce: “Wannan shiri ana aiwatar da shi ne tare da cikakken haɗin gwiwa da gwamnatocin jihohi a matsayin wata kyakkyawar shaida tare da nunin cewa mai girma Shugaban Ƙasa ya sadaukar da kan sa wajen yin aiki kafaɗa da kafaɗa da dukkan matakan gwamnatoci don tunkarar matsalar fatara da yunwa wadda ta zama babban ƙalubalen gina ƙasa da mu ke fuskanta a yau.

“Mun taru a nan ne a yau domin ƙaddamar da shirin Ba Da Lamuni Ga Mutane Mabuƙata (GVG) a Bauchi, Azare da Darazo.

“Shirin na GVG shiri ne na cika alƙawarin Manufofin Buhari ga dukkan mutane mabuƙata, domin a ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen Gwamnatin Shugaba Buhari ga kan talakawa, wanda ya yi daidai da tsarin sa na tausayawa na tsamo ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga fatara da yunwa a cikin shekara out.”

An ɗauki ma’aikata ‘yan sa ido kan shirin su 380 waɗanda ake kira ‘Independent Monitors’, kuma an ba su takardun kama aiki nan-take tare da na’urori na musamman da za su yi aikin sa-idon da su domin inganta aikin su.

Bugu da ƙari, an tsara bai wa ‘yan gudun hijira mutum 600 kuɗi N50,000 kowannen su, waɗanda a cikin su akwai naƙasassu da tsofaffi.

Hajiya Sadiya ta ƙara da cewa, “Za a biya kuɗin agaji N50,000 sau ɗaya ga kowane ɗan gudun hijira a ƙarƙashin shirin Agaji da Haɓaka Rayuwar Matasa, wato ‘Youth Empowerment and Social Support Operations’ (YESSO), wanda manufar sa ita ce a inganta ƙwarewar su a ayyukan kasuwanci domin sama wa kai aikin yi, sama wa kai dukiya da kuma sama wa wasu daban aikin yi.

“A Jihar Bauchi, masu cin moriyar shirin mutum 600 ne za a ba agajin tsabar kuɗi N50,000 kowannen su.”

A taron, an ƙaddamar da komfutar biyan kuɗi ta shirin Bayar da Tsabar Kuɗi Bisa Sharuɗɗa, wato ‘Conditional Cash Transfer (CCT) Programme’.

A cewar mai tallafa wa ministar a fagen aikin jarida, Miss Nneka Ikem Anibeze, muhimmancin wannan shiri shi ne a samar da matattarar bayanai mai inganci, ta gaskiya, kuma mai sauƙin sarrafawa domin biyan kuɗaɗe ga masu cin moriyar shirin na Bayar da Kuɗi Bisa Sharuɗɗa, wato ‘Conditional Cash Transfer (CCT) Programme’.

Leave a Reply