Muna cikin fitinar maza

0
65

Matar da abokin mijinta ya matsa mata.

Ta bayyana mana irin halin da ta samu kanta a ciki lokacin da abokin mijinta ya dage a kan sai ya yi lalata da ita.

Rabi ta ce “Ya fara ne da baiwa mijina kyaututtika ya kawo min tun daga ranar wata Juma’a da mijina ya gayyace shi cin abinci irin wanda amarya ke girkawa ango da abokansa.

Ba zan ce ga inda ya samu lambata ba har ya kira ni a wani yammaci ina kicin ina dafa abincin dare.

Koda na ji muryar namiji kuma ba ta mijina ba sai na tambaya ko wane?

Sai ya ce wane ne abokin mijinki, ya ambaci sunansa, wai ya kira ne ya ji ko yana gida? Sai bayan na amsa da cewa baya nan muka yi sallama sannan na soma tunanin inda ya samu lambata.

Mijina bai damu ba lokacin da na faɗa masa cewar abokinsa ya kira ni. Sai ma ya ce wai yana zaton ya taɓa amfani da wayarsa ne ya kira ni.

Rabi’atu ta ce ya yi ta zuwa gidanta da sunan ya zo wurin mijinta wanda kuma ya sani sarai mijin ba ya nan, sai ya ɗauki kuɗi ya ba ta masu tsoka ya ce ba sai ta nunawa mijin ba.
Sannan ya na taimakon mijin kasancewar ya fi mijinta ƙarfi.

Ya samu damar fita da ita motarsa ne lokacin da ta ke laulayin ciki kuma mijin ba ya gari.

Ina kwance ƙanwata da ke taya ni zama kasancewar baya nan ita ce ta kira shi ta faɗa masa cewa jikina ya yi zafi. Shi ne ya kira wannan abokin nasa ya faɗa masa. Sai ga shi da mota zai kai ni asibiti. Ya ce wa ƙanwata wai ta zauna ta dafa min abinci. kafin mu dawo.

Ta ci gaba da cewa “A zuciyata ban so haka ba amma ba ni da ƙarfin da zan yi magana, haka ta saka ni a motarsa muka tafi asibiti.

Ansa min ruwa da allurai haka ya tsaya kai na ya na ƙare min kallo sai faman kama min hannu da dafa min goshi yake yi.

Da ruwan ya ƙare sai muka nufo gida, ya tsaya Super market ya yi min siyayya sannan ya maido ni gida.

Washe gari na ɗan ji ƙarfin jikina, sai ga shi ya zo wai ya kai ni allura. To fa a wannan rana muka sha artabu domin bayan an min allurar wai bari ya kai ni ya kama min ɗaki a Hotel wai in samu isasshen bacci.

Na ce Allah ya tsari gatari da saran shuka. Ai na gane nufinka tun ba yau ba, na bar ka ne don bana son in haɗa ka da abokinka. Sai dai yanzu an zo maƙura, dole ya san komai. To in rage miki zance ba sai ya riga ni kiransa ba, ya ce masa “don Allah ka daina saka ni a sabgar gidanka, matarka ta na son jifana da mugun zato.”

Mijina ya kira ya na ta faɗa ya ƙi sauraro na yana zargin zan raba abotarsu.
Ƙarshe dai sai da ya dawo sannan na faɗa masa komi, da ƙyar na ɗarsawa zuciyarsa zargin abokin dan bai gama yarda ba. Na dai samu na cusa zargin abokin a zuciyarsa. Shi kuma abokin na samu ya fita harka ta.

Leave a Reply