Mutum 2,292 sun mutu a cikin haɗarurruka 5,066 a faɗin ƙasarnan.

0
162

 

Hukumar kiyaye haɗura ta Ƙasa (FRSC) ta ce mutane 2,292 ne suka mutu a hatsa mota 5,066 da suka auku tsakanin watan Janairu zuwa Yuni a faɗin Ƙasar nan.

Jami’in kula da ilimin Jama’a na Corps, Mista Bisi Kazeem ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da manema Labarai a ranar Juma’a 30/7/2022 a Birnin Tarayya a Abuja.

Kazeem ya ce mutane 33,424 ne suka yi hatsarin yayin da 16,333 suka samu raunuka daban-daban.

Ya ce adadin haɗuran (5,066) ya yi ƙasa da 5,320 da aka samu a shekarar 2021.

“Yawancin waɗanda suka samu raunuka tsakanin watan Janairu da Yuni a faɗin ƙasar sun wakilci
ragowar kusan kashi 10 cikin ɗari idan aka kwatanta da 17,903 da aka samu a lokaci guda
a 2021, “in ji shi.

Kazeem ya ce Hukumar ta FRSC ta kama jimillar mutane 312,279 daga watan Janairu zuwa watan Yuni bisa laifin aikata laifuka 344,182.

Ya kuma ɗora alhakin haɗuran kan tituna a kan gudu, tukin dare da kuma rashin haƙuri. Sannan ya buƙaci direbobin da su riƙa hutawa sosai kafin su fara duk wata tafiya.

Ya kuma shawarci masu ababen hawa da su rage tafiye-tafiyen dare, inda ya kara da cewa galibin haɗurran da ke haddasa mace-macen suna faruwa ne cikin dare.

Jami’in ya ce hukumar ta FRSC za ta ci gaba da wayar da kan masu ruwa da tsaki akan lamarin
tuki lafiya. Yayin da ake tsananta aiwatar da dokokin kiyaye hanya.

Ya ce Rundunar za ta inganta haɗin gwiwa da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da zirga-zirgar ababen hawa da kuma kariya ga Manajojin motoci.

Kazeem ya yi kira ga masu amfani da hanyar da su bi duk ƙa’idojin zirga-zirga.

Leave a Reply