Na sauka daga takara bana cikin masu neman wannan kujera ba na tare da wannan Jam’iyya ta ADP

0
87
Dan takara Aminu Ladan Abubakar Alan waka

Basarake kuma dan siyasa Aminu Ladan Abubakar wanda aka fi sani da Alan waka ya janye daga wannan Jam’iyyar sa ta ADP daga takarar sa ta dan majalisar Nasarawa tare da barin Jam’iyya ADP. gaba daya.

Ala ya bayyana janye war sa daga kujerar a ranar 1 ga watan Janairun 2023, da ya ke bayani, ya ce yanayi ne yasa ya bayyana a matsayin dan takara haka kuma yanayi ne yasa shi janyewa daga takara.

Da ya ke bayani a shafin sa na YouTube Ala ya bayyana hakan a matsayin kaddara kasanceawar shi musulmi, kuma ya yi jinjina ga jagororin shi na tafiyar in da ya ce ko ba komai ya samu ilmi da ya kasance a cikin takarar tsundum maimakon hangen ta daga nesa da yake yi a baya.

Ala ya kara da cewa yadda ya shelanta cewa ya na takara a Kafafen yada labarai, haka kuma yanzu yake shelanta janye war sa daga takara bisa ga dalilin shi na rashin mallakar takardar shedar cewa shi din dan takara ne.

Aminu Ladan Abubakar Alan waka

Ya kara da cewa zabe ya rage saura kwana 55 amma bashi da wata kwakkwarar sheda da zai nuna cewa shi dan takara ne a Jam”iyyar da ya ke ikrari.

Anyi Alkawura za a bamu kujeru a Jami’iyar ADP karkashi kungiyar mu ta 13+13 amma tun daga lokacin ban kuma jinwani motsi ba, ita kanta 13+13 banga ta yi wani yunkuri ba a matsayin mu ‘ya”yanta muna takara har zuwa yau.

Aminu Ala ya ci gaba da cewa labari muke ji daga wasu mutane wadan da ba su da cikakken hurumi, domin Jam’ iyya ke da hurumin bada sunan dan takara ga INEC sannan INEC ta sanar wa ‘yan kasa sunan dan takarar da Jam’ iyyar ta tsayar. To har zuwa yau da ya rage saura kwana 55 a kada kuri a bamu samu wata alama ko daya ba.

Amina Ladan Abubakar Alan waka

Ala ya ce duba da wannan yasa na dauki Alkalami na rubuta takardar sauka daga takara, dan bana son in karya dokar Jam’iyya ko ta INEC, ko ta kasa.

Na rubuta takarda na kai tun daga karamar hukuma har zuwa jiha da kasa da duk mai ruwa da tsaki a Jam’iyya ADP cewa Ni Aminu Aminu Ladan Abubakar Alan waka, na sauka daga takara bana cikin masu neman wannan kujera ta Nasawa Constituency ba na tare da wannan Jam’iyya ta ADP.

Na sauka bisa alkawarin da mukayi da su na cewa za su bamu kujera mu tsaya takara muka shiga wannan Jam’iyya to wannan alkawarin bai cika ba.

Aminu Ladan ya kara da cewa ba wani ne ya masa laifi ba ya lura da kurewar lokacin ne kuma ba wata tartibiyar magana, ya yi ikirarin cewa kamala da cikar mutuncin sa suka sa aka tsaida shi a matsayin dan takara, don haka baya son ya yi Abinda zai taka doka ta shara’a bare har ya zuba da kimar sa kasanceawar sa jariri dan takara.

Yace ya samu ilmi duk da ingiza mai katu ruwa da aka yi masa a tafiyar ban da gurin kaddamar da takara babu inda ake ganin sa.  An mayar da ni kamar wani alon sha, ya kara da cewa har gara ma allon sha za a dakko a yi rubutu a wanke a mayar a jingine.
To ni kamar allo mara amfani aka mayar dani bana sani komai, haka na tashi a wannan Jam’iyya, amma da sun san ayyukan da na yi a karkashin kasa da susan cewa  sunyi babbar asara na rabuwa da wannan tsayayyen dan takara daga Nasarawa.
Ya yi kira ga Kungiyoyi da  suka mara masa baya da cewa, karsu damu za su zauna su yi taro su duba inda ya kamata so koma dan a gudu tare a tsira tare. Ya kuma yi musu godiya bisa gayon baya dari bisa dari da suka ba shi.

Leave a Reply