Nijeriya na so ƙasashe su haɗa gwiwa su tunkari matsalolin gudun hijira da shige-da-fice

0
68
Hajiya Sadiya Umar Farouq a wajen taron na UNHCR

 

 

DAGA WAKILIN MU

Nijeriya ta yi kira ga sauran ƙasashe da su haɗa kai wajen neman hanyoyin magance matsalolin da su ka danganci shige-da-fice da gudun hijira.

Ministar Harkokin Jinƙa,  Agaji Da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ce ta yi wannan kiran a jawabin da ta gabatar a ranar Litinin a wajen Taro na 73 na Babban Kwamitin Gudanarwa na Kwamishinan Hukumar ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHCR) a birnin Geneva.

Mai tallafa wa ministar a aikin jarida, Miss Nneka Ikem Anibeze, ta ruwaito cewa Hajiya Sadiya ta bayyana irin ƙoƙari da kuma da tsare-tsaren da gwamnatin Nijeriya ta ke fito da su domin inganta ayyukan agaji a Nijeriya musamman ma kan batun ‘yan gudun hijira da masu shige-da-fice tsakanin ƙasashe da kuma ‘yan gudun hijira na cikin ƙasa.

Ministar ta yi kira ga ƙasashe masu ruwa da tsaki a lamarin da su guji nuna bambanci da wariyar launin fata domin gina zaman lafiya mai ɗorewa tare da inganta hanyoyin samun abinci ga al’umma mabuƙata.

Ta ce: “Nijeriya ta na kira ga ƙasashe da su haɗa gwiwa tare da haɗa kai da ɗaukar nauyi da zama tsintsiya maɗaurin ki ɗaya musamman a kan yadda matsalar ke shafar ƙasashe inda ‘yan gudun hijira ke fitowa da ƙasashen da ke karɓar su. Wannan ya yi daidai da sadaukarwar mu a matsayin membobin Yarjejeniyar Ƙasashe Kan ‘Yan Gudun Hijira.

“Nijeriya ta yabi ƙoƙarin UNHCR. Mu na kuma kira ga UNHCR da sauran masu ruwa da tsaki kan batun shige-da-fice da su ci gaba da su haɗa hannu da gwamnatin Nijeriya domin a daidaita tsare-tsare da manufofin mu na cigaban ƙasa da muradan ta.

“Matsalar da ake samu daga sauyin yanayi a Fadamar Tafkin Chadi ta haifar da ƙarin yawan mutanen da aka tilasta wa barin yankin.”

Ta lura da cewa a cikin ‘yan lokutan nan ambaliya da sauran manyan al’amuran sauyin yanayi sun ba da gudunmawa ga ƙaruwar ‘yan gudun hijira.

Ta ce, “A namu ɓangaren na gwamnati, mu na aiwatar da Shirin Ko-ta-kwana na Samar da Abincin Gaggawa domin inganta shiryawa da ƙarfafawa ga al’umma kamar yadda aka tsara a Tsarin Sendai.”

Hajiya Sadiya ta ce: “Mu na neman a haɗa gwiwa domin a rage tare da shirya zama da sauyin yanayi musamman a wajen batun tilasta wa mutane barin waje.

“Wariyar launin fata da nuna bambanci ba abubuwa ne da za a bar su su samu gindin zama a duniyar mu ta yau ba idan har mu na so mu gina zaman lafiya mai ɗorewa, samar da arziki da kuma inganta sana’o’i da juriya ta yadda za a kyautata ƙasa tare da kare al’umma marasa ƙarfi.”

A ƙarƙashin Yarjejeniya Uku da aka rattaba tsakanin Nijeriya, Kamaru da UNHCR, sama da ‘yan gudun hijira 5,000 ‘yan Nijeriya aka sake dawowa da su cikin ƙasar su bisa amincewar su.

Ta ce a cikin shekaru shidda da su ka gabata, Nijeriya ta samu ƙarin yawaitar masu neman mafaka da ‘yan gudun hijira daga ƙasashe da ke maƙwabtaka da mu.

Yanzu haka Nijeriya ta na mai masaukin baƙi na ‘yan gudun hijira su 84,314 da masu neman mafaka daga ƙasashe sama da 34, ga kuma ƙarin sama da ‘yan gudun hijira 5,000 daga Kamaru waɗanda ba su da rajista, waɗanda su ka iso kwanan nan.

“Akwai ‘yan gudun hijira ‘yan Nijeriya kimanin 341,642 a ƙasashen Nijar, Chadi da Kamaru,” inji ta.

Leave a Reply