Obasanjo: DUK WANDA YA CE NIGERIA ANA JIN DAƊI KO TA GYARU YA KAMATA A BINCI KWAKWALWARSA.

0
157

 

 

Tsohon shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya ce har yanzu Najeriya ba ta cimma burinta ba.

A cewar Obasanjo, duk wanda ya ce al’amura suna da kyau kamar yadda suke a yanzu, to a duba kansa.

Obasanjo ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba a wajen taron shekara-shekara na Wilson Badejo Foundation karo na 15 a Legas.

“Najeriya bata inda ya kamata ta kasance a yau. Idan wani ya ce babu laifi a inda muke a halin yanzu, to ana bukatar a duba kwakwalwar mutumin,” in ji tsohon shugaban.

A cewar Obasanjo, dole ne ‘yan Najeriya su zaɓi ɗan takarar da ya dace a 2023 domin ci gaban ƙasar domin ta na cikin haɗari.

“Ko dai mu yi zabin da ya dace a 2023 domin idan muka yi zabi mai kyau, za mu isa can,” in ji shi.

“Duk da haka, idan bamu yi zaɓin da ya dace ba a 2023, abubuwa za su cinye mu kuma yakamata muyi addu’a a kan wannan. Dole ne mu yi zabi mai kyau a 2023.

“Abokina, marigayi Ahmed Joda, ya kasance yana gaya min cewa Allah Yabamu duk abin da al’umma ke bukata kuma babu bukatar addu’a domin idan Allah Yabaka komai kuma ka yi almubazzaranci, to ansamu matsala.

“Na gaya masa cewa ko da a haka har yanzu muna bukatar addu’a a matsayinmu na al’umma domin abin da yake mai kyau yana bukatar addu’a sannan kuma a ɗaya bangaren ma, muna bukatar ƙarin addu’o’i.

A watan Mayu, Obasanjo ya ce Najeriya na bukatar Shugaba mai kishin ƙasar.

Tsohon shugaban ƙasar ya ce halin da ƙasar ke ciki yana da ban tausayi a gare shi da sauran ‘yan Najeriya, amma duk yadda lamarin Najeriya ya yi tsanani, ‘yan ƙasa ne kawai za su iya gyara lamarin.

Leave a Reply