Gaga Abu Usaimin
Farfesa Florence Obi,, shugaban jami’ar Calaba ya ja hankalin sababbin ɗaliban da jami’ar ta ɗauka da su miƙa duk wani rahoto na cin zarafi da haikewa daga malaman jami’ar ko ma’aikatanta.
Obi ya yi kiran ne a yayin da ake gudanar da taron wayar da kai wanda aka shirya wa sababbin ɗaliban da jami’ar ta ba wa gurbin karatu a wannan shekarar.
A cewarta shugabancinta ba zai ƙyale duk wani keta haddi ko nuna bambanci jinsin ga mata ba.
Ta ƙara da cewa za su samar da cibiyar wayar da kai da kuma bayar da shawarwari a kan jinsi.
A yayin da take ƙarfafa wa mata guiwa domin su miƙa rahoton keta haddi da cin zarafi, ta kuma janyo hankalinsu wurin yin shiga tagari da kauce wa fitsara yayin mu’amala da malamai da ma’aikata maza.
“Ya ku ɗalibaina, musamman ma matan cikinku, ina mai ba ku ƙwarin guiwar kawo ƙorafin keta haddi ko cin zarafin da kuka fuskanta daga malamai da kuma ma’aikata. Kada ku bari wani ya ruɗe da maki don ya cim ma muradinsa. Mun samar da tsari mai kyau don kare martabar hazaƙar ɗalibi, babu wani malami da zai kayar da ɗalibi mai ƙoƙari.
Ɗalibai maza ku ƙaurace wa miyagun ƙungiyoyi, don su ke janyowa a faɗa ƙungiyar asiri. Ku mai da hankali sosai a kan karatu, zangon karatu na farko taƙaitacce ne sakamakon yajin aikin da ƙungiyar malamai ta yi (ASUU).
Domin zama cikakken ɗalibi dole sai ka yi rijista da makaranta, tun daga kan biyan kuɗin makaranta har rijistar darussan da za a yi. Za a yi rijistar ne ta yanar gizo, don haka kada ka sake ka ba wa wani kuɗinka, duk biyan kuɗi ta banki za a yi shi.”
Shugabar ta nemi ɗaliban da su zama a ankare, kum su sa ido sosai, sannan kuma su ƙaurace wa wurare masu haɗari.
A baya-baya nan ne shugaban harkokin ɗalibai na makarantar ya ja hankalin ɗalibai a kan mayar da hankali kan karatu. Domin sakamakon shekarar farko shi ne yake bayuwa zuwa ga sakamakon ƙarshe na makaranta. Sannan ya nemi su ƙaurace wa tarukan da za su kawar musu da hankali daga bayar karatu.